Hoto: An kamasu sun yiwa matar aure da kawayenta fyade
Hukumar 'yansanda sun kama wadannan 'yan fashin a Abagana dake karamar hukumar Njikoka jihar Anambra.
Rahoto yace mutanen sanannun masu yiwa mata fyadene.
Sun shiga gidan wata mata inda suka sameta ita da kawayenta suka musu fyade sannan suka sa daya daga ciki ta tura musu kudi.
Kakakin 'Yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wanda ake zargin sun amsa laifukansu.
Sannan za'a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.