‘Yan Bindiga sun kashe mutane 12 ciki hadda ‘yansanda 7 a jihar Zamfara
A ranar Alhamis, 'yan Bindiga sun kai hari garin Magarya dake karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara inda suka kashe mutane 12 ciki hadda 'yansanda 7.
A cikin wadanda aka kashe din akwai daya daga cikin Askarawan Zamfara, da kuma mutane 4 daga kauyen.
Kwamishinan 'yansandan jihar, Muhammed Shehu Dalijan ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yace 'yan Bindigar sun kai harinne akan mashina au kusan 300 inda suka zagaye 'yansandan suka bude musu wuta suka kashe 7 da jikkata da yawa daga ciki.
Ya kara da cewa, 'yan Bindigar sun ji haushine 'yansanda sun hanasu kai hari kauyen shekaru 2 tun bayan da aka kaisu kauyen.
Saidai yace zasu kara yawan 'yansanda a garin.
'Yan Bindigar dai sun kone gidaje 2 da mota daya da sauran wasu abubuwa.