Friday, December 13
Shadow

Jihar Naija

Gwamnin ban tausai:Ji yanda mutane suka nutse a ruwa yayin da suka shiga kwale-kwale dan tserewa harin ‘yan Bin-di-ga a jihar Naina

Gwamnin ban tausai:Ji yanda mutane suka nutse a ruwa yayin da suka shiga kwale-kwale dan tserewa harin ‘yan Bin-di-ga a jihar Naina

Duk Labarai, Jihar Naija, Tsaro
Mutane aun nutse a ruwa yayin da suka shiga jirgin ruwa dan tserewa harin 'yan Bindiga a garin Gurmana dake karamar hukumar Shirori jihar Naija. Yawanci idan maharan suka kai hari, mutane kan tsere zuwa wani tsibiri har sai kura ta lafa kamin su koma gidajensu. Mutanen daai sun tserene ranar Laraba. Saidai ranar Alhamis, yayin da suke dawowa daga kan tsibirin da suka samu mafaka, mutane 4 sun mutu, bayan da jirgin ruwan da suke ciki yayi hadari.
Kalli Hotuna: Yanda ‘yan B0k0 Hqrqm suka yanka mutane 7 a Bassa da Erena dake jihar Naija

Kalli Hotuna: Yanda ‘yan B0k0 Hqrqm suka yanka mutane 7 a Bassa da Erena dake jihar Naija

Jihar Naija, Tsaro
Rahotanni daga Bassa da Erena a jihar Naija na cewa mayakan kungiyar B0k0 Hqrqm sun kai mummunan hari a yankin. Majiyar Hutudole tace an kai harinne a garin Makuba Lantan Bakin Kogi Bassa inda aka kashe mutane 7 ta hanyar yi musu yankan rago. Harin ya farune a jiya, Alhamis kamar yanda majiyar tamu ta tabbatar. Masu fada a ji a yankin sun nemi mahukunta da su kaiwa mutanen yankin musamman wadanda suka rasa muhallansu dauki. Mun samu hoton kan daya daga cikin mutanen da aka yanke, Allah ya kyauta.
Ƙasa ta rufe mutum 30 a mahaƙar ma’adanai ta jihar Neja

Ƙasa ta rufe mutum 30 a mahaƙar ma’adanai ta jihar Neja

Jihar Naija
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja a Najeriya (NSEMA) ta ce kimanin mutum 30 ne ake fargabar sun mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta auku a wani wurin hakar ma’adinai. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Galkogo na ƙaramar hukumar Shiroro. Hukumar ta ce an kuma samu nasarar ceto mutum shida da rai, sai dai sun samu munanan raunuka. Mahakar dai ta rufta ne a jiya Litinin lokacin da suke tsaka da aiki haƙar ma'adanai. Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Zubairu Ahmad:
‘Yan Bindiga sun kashe mutane 7 da sace 150 a Munya jihar Naija saidai an kashe ‘yan Bindigar guda 25

‘Yan Bindiga sun kashe mutane 7 da sace 150 a Munya jihar Naija saidai an kashe ‘yan Bindigar guda 25

Duk Labarai, Jihar Naija
Shugaban karamar Hukumar Munya ta jihar Naija, Malan Aminu Najume ya koka kan ayyukan ‘yan Bindiga a karamar hukumar tasa inda ya nemi a kubutar da mutanensa daga hannun ‘yan Bindiga. Ya bayyana hakane ga manema labarai inda yace ‘yan Bindigar sun shiga garin kuci inda suka kashe mutane 7 da kuma sace 150. Ya bayyana cewa, cikin wadanda aka kashe akwai jami’an tsaro 4 da kuma ‘yan Bijilante da wasu mutanen garin. Saidai ya jinjinawa jami’an tsaron dake garin inda yace aun kashe guda 25 daga cikin ‘yan Bindigar. Yace yawanci ‘yan Bindigar na zuwa ne daga jihar Kaduna inda suke musu aika-aika daga bisani su koma Kadunar. Yace sun shiga garin da mashina kusan 100 kuma sun rika bi gida-gida suna daukar wanda suke son yin garkuwa dasu da suka hada da mata.