Wednesday, January 15
Shadow

Kannywood

Ni yanzu bakin Jini gareni>>Haruna Talle Mai fata

Ni yanzu bakin Jini gareni>>Haruna Talle Mai fata

Kannywood
Tauraron Fina-finan Hausa, Haruna Talle Mai fata ya bayyana cewa, shi a yanzu bakin jini gareshi inda yace yanzu babu budurwar dake sonsa. https://twitter.com/el_uthmaan/status/1843007673274671269?t=DO5MOmksGRY4LauMyae3gw&s=19 Ya bayyana hakane a hirar da abokiyar aikinsa, Hadiza Gabon ta yi dashi a shirinta na shafin Youtube. Talle ya bayyana abubuwan da suka dauki hankali a cikin hirar tasu ciki hadda inda yake cewa yayi nadamar barin sana'ar fata ya koma harkar fim.
Kalli Bidiyon karya da ya nuna Momi Gombe da Umar M. Sharif sun Rungumi Juna

Kalli Bidiyon karya da ya nuna Momi Gombe da Umar M. Sharif sun Rungumi Juna

Umar M. Sharif
Wani Bidiyo na karya wanda aka yi Editing ya nuna yanda Wai mawaki Umar M. Sharif da abokiyar aikinsa,Momi Gombe sun rungumi juna. Bidiyon dai ya dauki hankulan mutane sosai a kafafen sada zumunta saidai da yawa sun fahimci cewa karyane. https://www.tiktok.com/@m.o.m.e.e.gombe/video/7410853116750335238?_t=8pc3cJSaebm&_r=1 A wannan zamani dai ana amfani da fasahar AI wajan hada abubuwan da a baya ake ganin kamar ba zasu iya haduwa ba.
Ji Martanin da Hadiza Gabon tawa wani da yace mata ta bashi kudi

Ji Martanin da Hadiza Gabon tawa wani da yace mata ta bashi kudi

Duk Labarai, Hadiza Gabon
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta wallafa wannan hoton nata a shafinta na sada zumunta inda masoyanya suka rika yabawa. Saidai wani ya roketa da ta yiwa mutane kyautar kudi kamar yanda dan siyasa na jihar Kaduna,Bello ElRufai ke yi. Saidai Hadizar ta mai martanin cewa, ya je ya samu aikin yi. Ya dai mayar mata da martanin cewa, ko ya kawo takardunsa ta bashi aiki a dakin hada shirye-shiryenta na Youtube? Daga nan dai Hadizar bata sake takashi ba. A baya dai, Abokiyar aikin Hadizar, Rahama Sadau ta rabawa masoyanta kudade ta shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram.
Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa, yayar mahaifiyar jarumar masana’antar Kannywood, A’isha Humaira, ràsųwa a birnin Maiduguri

Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa, yayar mahaifiyar jarumar masana’antar Kannywood, A’isha Humaira, ràsųwa a birnin Maiduguri

Kannywood
INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRAJI'UN Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa, yayar mahaifiyar jarumar masana'antar Kannywood, A'isha Humaira, ràsųwa a birnin Maiduguri. Humaira ta bayyana rasuwar a shafinta na Instagram inda ta nemi al'ummar musulmi da su sanya ta cikin addu'a Allah Ya gafarta mata tare da sauran al'ummar Annabi (S.A.W) da suka riga mu gidan gaskiya. Za a yi mata sallar Jana'iza a gobe da safe, a birnin Maiduguri na Jihar Borno.