Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wadannan hotunan wanda aka dauka daga wajan bikin zagayowar ranar Haihuwarta da ta yi jiya.
Hadiza ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta inda ta cika shekara 35 da haihuwa.
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wannan hoton nata inda take tare da abokin aikinta dan kasar India.
Ta saka hoton a shafinta na sada zumunta:
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta saki wannan hoton inda ta yi godiya ga masoyanta da suka tayata murnar zagayowar ranar Haihuwarta.
A jiya ne dai Hadiza Gabon ta yi murnar zagayowar ranar Haihuwarta inda tace ta cika shekaru 35 da Haihuwa.
Tauraron mawakin Hausa, Ali Jita ya halarci Filin Wembley dake birnin Landan kasar Ingila da yammacin jiya inda aka buga wasan karshe na gasar Champions League tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund.
Jiya ya wallafa bidiyo da hotunansa a cikin filin wasan a shafukansa na sada zumunta:
https://twitter.com/alijitaa/status/1796981621461025021?t=OU25PygGuJxpRFuRPbBLGw&s=19
Wata sabuwar Jaruma a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Muhammad Sani ta bayyana Kannywood ɗin a matsayin wata masana'anta wacce ake faɗakarwa da gyaran tarbiyyar al'umma ba wai ɓata tarbiyya ba.
Maryam ta bayyana haka ne ta cikin wata tattaunawarta da Jaridar Dokin Ƙarfe TV inda ta ƙara da cewa "Na shigo masana'antar Kannywood ne domin ina da gudunmawar da zan bayar game da gyaran tarbiyyar al'ummar nan tamu". In jita.
Maryam ta kuma ƙara da cewa "Bai kamata mutane suna ƙyamatar ƴan fim ba. Domin fim harka ce ta kawo cigaba da magance matsalar tsaro da raya al'adun Hausa Fulani". A cewar ta.
Daga ƙarshe Malama Maryam ta kuma ƙara da cewa tarbiyya tana farawa ne tun daga gida, dan haka masana'antar Kannywood waje ne na koya tarbiyya ba ɓatawa ba". In ji ta....
Tauraron Fina-finan Hausa kuma Mawaki, Garzali Miko yayi tambayar wai ta yaya mutum zai san ya haukace?
Yayi tambayar ne a shafinsa na sada zumuntar Instagram.
Tauraron Mawakin Hausa, Ado Gwanja kenan a wannan hoton nasa a cikin gidansa na Alfarma.
Ado ya saka hoton a shafinsa na sada zumunta inda yake bada shawarar a rika jure damuwa.
Taurarin Fina-finan Hausa, Rahama Sadau da Ali Jita kenan a wadannan hotunan da bidiyo suke shakatawa a kasar waje.
An ga Jita da Rahama dai suna nishadi tare a cikin mota da kan titi.
Ali Jita ne ya saka bidiyon a shafinsa na sada zumunta.
https://www.tiktok.com/@realalijita/video/7375206383370652933?_t=8mpctjMHVyA&_r=1
Da yawan mata da maza na masana'antar Kannywood sukan je kasashen waje dan shakatawa.
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta yi murnar zagayowar ranar haihuwarta inda tace ta cika shekaru 35.
Hadiza ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda kuma masoya da abokan arziki suka yi ta tayata murna.
Da yawa dai masu murnar ranar haihuwarsu basu cika bayyana shekarunsu ba, amma Hadiza Gabon ta yi ta maza ta bayyana cewa shekarunta 35.
Ko da yake a hakan ma wasu da yawa sukan karyata.
Daga cikin abokan aikin Hadiza Gabon:
Shamsu Dan iya ya tayata Murna inda ya saka hotonsu tare a shafinsa da yi mata fatan Alheri:
Sauran wanda suka taya Hadiza Gabon murna sun hada da Dj Abba, Hassan Giggs, da dai sauransu.