Thursday, January 16
Shadow

Kano

Da Duminsa: ‘Yansanda sun haramta hawan Sallah a Kano

Da Duminsa: ‘Yansanda sun haramta hawan Sallah a Kano

Kano
Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kano ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al'ada a faɗin jihar. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan babbar sallah da za a soma ranar Lahadi. Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami'anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a jihar, kafin sallah da lokacin bukukuwan bayan sallar. ''Haka kuma an haramta duka nau'ikan hawan sallah a lokacin bukukuwan babbar sallah da ke tafe'', in ji sanarwar. 'Yan sandan sun ce sun ɗauki matakin ne sakamakon rahotonnin tsaro da suka samu da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al'ummar ji...
Iyalan Sheikh Ibrahim Nyass, sun yi kira ga Muhammadu Sanusi II yayi koyi da sawun Kakan sa Muhammad Sanusi l da aka cire ya hakura

Iyalan Sheikh Ibrahim Nyass, sun yi kira ga Muhammadu Sanusi II yayi koyi da sawun Kakan sa Muhammad Sanusi l da aka cire ya hakura

Kano
Shugaban Darikar Tijjaniyya Mahi Nyass ya shawarci Lamido Sanusi da ya yi koyi da kakansa ta hanyar kin amincewa da kujerar sarautar Sarkin Kano. Sarki Sanusi shi ne jagoran kungiyar Tijjaniyya a Najeriya. An mayar da shi a matsayin Sarkin Kano a karshen watan da ya gabata bayan da Gwamnatin Jihar ta yi wa dokar masarautu gyara inda ta rusa masarautu hudu daga cikin biyar da ke Jihar tare da tube Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano. Mista Ado Bayero dai yana kalubalantar tsige shi ne a gaban kotu, kuma yanzu haka yana zaune a karamar fadar Sarkin bisa kin amincewa da umarnin Gwamnatin Jihar. Sai dai kungiyar ta Islama a wata takarda mai dauke da kwanan watan 3 ga watan Yuni mai dauke da sa hannun babban shugabanta Mista Nyass ta bukaci Sanusi da ya ki amincewa da mayar da shi ...
Ji wata murya da aka ce ta Sarki Sanusi ce tana cewa zasu sauke Gwamna Abba Gida-Gida, “Gara Ganduje ya dawo”

Ji wata murya da aka ce ta Sarki Sanusi ce tana cewa zasu sauke Gwamna Abba Gida-Gida, “Gara Ganduje ya dawo”

Kano
Wata murya data bayyana a kafafen sada zumunta wadda ake cewa ta me martaba sarkin Kano ce, Muhammad Sanusi II ta rika cewa ba'a musu abinda suke so ba. Sannan kuma zasu yi amfani da karfin jama'a su sauke Gwamna Abba Gida-Gida, an ji muryar na cewa, gara Ganduje ya dawo. Saidai babu wata kafa ko majiya me zaman kanta data tabbatar da cewa, wannan muryar ta sarki Muhammad Sanusi II ne. https://twitter.com/Engr_Alkasimfge/status/1800821908126249077?t=7lPi1Tm7EWRvndIKrHfiVw&s=19 Wannan murya tana iya yiyuwa kwaikwayon muryar sarkin aka yi, kamar yanda wasu ke zargi, ko kumama an yi amfani da fasahar zamani ta AI Voice wajan yinta. A Kano dai har yanzu akwai Sarki Muhammad Sanusi II wanda shine Gwamnatin jihar ta nada a matsayin sarki, sannan akwai Me marba Aminu Ado Baye...
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi

Kano, Siyasa
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi a faɗin jihar a wani mataki na farfaɗo da ɓangaren ilimin jihar. Yayin da yake jawabi a wani taro da gwamnatin jihar ta shiyya, gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ya ce matakin ya zama wajibi domin magance matsalolin da ɓangaren ilimin jihar ke fuskanta. Gwamnan ya kuma yi kira da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimin jihar su fito su haɗa ƙarfi domin magance matsalolin da suka yi wa ɓangaren ilimin jihar katutu. ''Ina Kira ga masu ruwa da tsaki da gwamnati da malamai da iyaye da kamfanoni masu zaman kansu da sauran al’umma, su haɗa kai, wajen farfaɗo da fannin ilimi, domin ci gaban al’ummarmu'''. ''Samun ilimi mai inganci shi ne babban makami mafi inganci na yaƙi da talauci da miyagun laifuka cikin al'ummarmu''. Gwamn...
A yau Juma’a wata kotun tarayya za ta saurari ƙarar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado ya shigar gabanta

A yau Juma’a wata kotun tarayya za ta saurari ƙarar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado ya shigar gabanta

Kano, Siyasa
Nan gaba a yau, Juma'a ne wata babbar kotun tarayya za ta saurari ƙarar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya shigar gabanta, inda yake neman kotun ta hana kama shi, sannan kuma a mayar da shi gidan sarki na ƙofar kudu. Cikin waɗanda sarkin ya shigar da su ƙarar har da ƴansanda da jami'an tsaro na civil defence. Ranar 28 ga watan Mayu mai shari'a Amobeda Simon ya bayar da umarnin cewa waɗanda ake ƙarar kada wanda ya hana shi shiga gidan sarki na kofar kudu ko hana shi amfani da duk wasu abubuwan da ya cancanta a matsayin sarki. Sannan umarnin kotun ya ce kada fitar da duk wanda yake cikin gidan sarki ba bisa ka'ida ba, har zuwa lokacin da kotun za ta saurari buƙatar da aka gabatar mata. A yau ne kuma kotun za ta zauna don sauraren ƙorafin da Sarkin, na 15 na Kano ya shigar. ...
Hotuna: Dan Gidan Sheik Dahiru Bauchi Ya Ziyarci Sarki Aminu Ado Bayero Tare Da Ba Shi Kyautar Alkyabba Da Carbi

Hotuna: Dan Gidan Sheik Dahiru Bauchi Ya Ziyarci Sarki Aminu Ado Bayero Tare Da Ba Shi Kyautar Alkyabba Da Carbi

Kano
Dan Gidan Sheik Dahiru Bauchi Ya Ziyarci Sarki Aminu Ado Bayero Tare Da Ba Shi Kyautar Alkyabba Da Carbi. Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi ya kaiwa Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ziyara tare da yi masa kyautar Alkyabba da carbi a yammacin yau a fadar shi dake Nasarawa. A yayin ziyarar yaja hankalin alumar Jihar Kano dasu zauna lafiya su bi doka, yakuma wuce zuwa hubbare domin yiwa Iyaye addua da ke kwance. Mai Martaba Sarki Alh. Aminu Ado Bayero ya bayyana jin dadin ziyarar girmamawar ya kuma godewa tawagar Sayyadi da kuma aiken gaisuwa ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi da addu'ar Allah Ya kara masa lafiya da nisan kwana. Daga Abdulwahab Sa'id Ahmad
WATA SABUWA: Babu Wanda Muka Yi Wa Mubaya’a Tsakanin Sarki Sanusi II Da Sarki Aminu Ado Bayero, Cewar Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi

WATA SABUWA: Babu Wanda Muka Yi Wa Mubaya’a Tsakanin Sarki Sanusi II Da Sarki Aminu Ado Bayero, Cewar Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi

Kano
WATA SABUWA: Babu Wanda Muka Yi Wa Mubaya'a Tsakanin Sarki Sanusi II Da Sarki Aminu Ado Bayero, Cewar Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi Sayyadi Muktar Ibrahim Dahiru Bauchi ya musanta labarin da wasu jaridu suka wallafa cewar sun je sun yi wa Sarki Sunusi II mubaya'a sannan suka kara yi wa Sarki Aminu Ado Bayero mubaya'a. A cewar sa sun kai ziyarar ne karkashin wata kungiya da Sheikh Aminu Dahiru Bauchi ke jagoranta na hadin kan al'umma musulmi tare da samar da cigaba, inda daga nan suka kuma kaiwa Sarki Aminu ziyara domin jajantawa akan abun da ya faru da shi. "Mu ba mu dauki bangare ba, kawai muna fatan Allah ya kawo dauki ne akan abun da ke faruwa a Kano, domin duk wani Musulmi a Arewa ba zai ji dadin abun da ke faruwa ba a Gidan Dabo", inji SayyadiMukhtar Ibrahim Sheik Dahiru Ba...
Masarautar Kano: Yajin aiki ya hana sauraron ƙarar Aminu Ado

Masarautar Kano: Yajin aiki ya hana sauraron ƙarar Aminu Ado

Kano
A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta fara a yau ya kawo cikas wajen zaman sauraron ƙarar da Alhaji Aminu Babba Danagundi ya shigar yana ƙalubalantar rushe masarautun jihar. Gwamna Abba Kabir ya soke masarautu biyar - ciki har da sababbi da aka ƙirƙiro a 2019 - bayan sauye-sauyen da Majalisar Dokokin Kano ta yi wa dokar masarautun jihar a watan Mayu, wanda hakan ya ba shi damar sauke Sarki Aminu Ado Bayero, kuma ya naɗa Muhammadu Sanusi II. Sai dai bayan ɗaukar matakin ne Aminu Ado Bayero ya koma garin kuma ya sauka a gidan sarki na Nassarawa saboda umarnin kotu da ya ce a dakatar da rushe masarautun har sai ta gama sauraron ƙarar. "Da zarar an janye yajin aiki kotu za ta ba mu sabuwar ranar sauraron ƙarar, umarnin da kotu ta bayar yana nan daram...

Ba za mu shiga yajin aiki ba – Ƙungiyar likitoci Kano

Kano
Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa reshen jihar Kano, (NMA), ta ce likitocin da ke aiki a asibitocin Kano za su ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ke gudanarwa. Sakataren ƙungiyar reshen jihar Kano, Dr Abdurrahman Ali, ya shaida wa jaridar Daily Trust ranar Litinin cewa " mu ƙwararru ne saboda haka ba a ƙarƙashin ƙungiyar ƙwadago muke kuma saboda haka ba za mu shiga yajin aiki ba". Ya ƙara da cewa “dukkannin likitoci da sauran ma'aikatan lafiya za su ci gaba da kasancewa a wuraren aikinsu. Bai zama lallai a cimma hakan ɗari bisa ɗari ba amma dai ba za mu shiga yajin aikn ba. E akwai yiwuwar ka je ka ga ma'aikacin da zai fito da fayil ɗinka ba ya nan amma kuma mambobinmu za su kasance a wuraren aikinsu.”