Wednesday, January 15
Shadow

Kano

Bidiyo Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Kano inda ake kone-konen Tayoyi

Bidiyo Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Kano inda ake kone-konen Tayoyi

Duk Labarai, Kano
Zanga-zanga ta barke a Kano kan rikicin sarautar da ya faru a jihar. An ga wasu matasa dauke da kwalaye inda suke ihun basa so. An kuma ga an kunnawa taya wuta a karkashin wata fastar Abba da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. https://twitter.com/daily_trust/status/1794756398351356238?t=lWt28qaBdF9DMh57LPzSgw&s=19 Daily Trust ta wallafa bidiyon wanda ya nuna abinda ke faruwa. A wani bidiyon kuma an ga matasan na kabbara: Jaridar dai tace matasan dake zanga-zanga suna neman a sake dawo da Sarki, Aminu Ado Bayero ne kan karagar Mulkin Kano: https://twitter.com/daily_trust/status/1794760364070187113?t=-yPmQeNl8DbliJ5gkTzO7Q&s=19 Lamari dai ya kazancene bayan da Aminu Ado Bayero ya dawo Kano kuma ya sauka a gidan sarki dake Nasarawa.
Abinda Gwamnatin Kano ta yi, Adalci ne kan rashin adalcin da aka min a baya>>Sarki Muhammad Sanusi II ya gayawa jami’an tsaro

Abinda Gwamnatin Kano ta yi, Adalci ne kan rashin adalcin da aka min a baya>>Sarki Muhammad Sanusi II ya gayawa jami’an tsaro

Duk Labarai, Kano
Me martaba Sarki Muhammad Sanusi II ya bayyanawa jami'an tsaro cewa abinda Gwamnatin jihar Kano ta yi na sauke Aminu Ado Bayero ta mayar dashi kan kujerar sarautar Kano, Adalci ne. Ya bayyana hakane a wani zama da suka yi shi da shuwagabannin jami'an tsaro na Sojoji, DSS, da 'yansanda. Jami'an tsaron sun bayyanawa sarkin cewa, akwai dokar data ce a dakatar da mayar dashi akan kujerar sarautar Kano. Saidai ya bayyana musu cewa, shi bai san da hakan ba, bai ma san da zaman kotun ba, kotun yanar gizo ce. A lokacin da ya karbi takardar sake nadashi sarautar Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa, dama a baya ya fada, Allah ne me bayar da mulki kuma ya karba a lokacin da ya so.
YANZU-YANZU: Kar ka jefa Kano cikin rikicin da ba za a iya gujewa ba, wasu Malaman Musulunci sun gargaɗi Gwamna Abba Kabir Yusuf

YANZU-YANZU: Kar ka jefa Kano cikin rikicin da ba za a iya gujewa ba, wasu Malaman Musulunci sun gargaɗi Gwamna Abba Kabir Yusuf

Duk Labarai, Kano
Malaman addinin Musulunci da Malaman addinin Musulunci a Jihar Kano, sun gargadi Gwamna Abba Yusuf da ya daina daukar duk wani mataki da zai jefa jihar cikin rikicin da ba za a iya kauce masa ba. Malaman da suka bayar da wannan shawara kan rikicin da ya barke a jihar, sun bayyana muhimmancin kaucewa yanke shawara da ka iya kawo cikas ga al’ummar jihar da kuma kara yiwa al’ummarta nauyi, wadanda tuni suka sha fama da munanan manufofin da suka gabata. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Khalifa Sheikh Lawi Atiku Sanka, Khalifa Mal Abdulkadir Ramadan, Farfesa Abdulahi Pakistan, Malam Yusuf Ahmad Gabari, Lawan Abubakar Triumph, Sheikh Mohd Bakari, Imam Usaini Yakubu Rano, Imam Jamilu Abubakar da Farfesa Ibrahim Mabushira suka sanya wa hannu. Malaman addinin Islama...
Duk Abunda ya faru a Kano, Tinubu ne sila>>Inji Atiku

Duk Abunda ya faru a Kano, Tinubu ne sila>>Inji Atiku

Duk Labarai, Kano
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan yaki ya barke a Kano to shugaban kasa, Tinubu ne sila. Atiku ya bayyana cewa dalili kuwa shine Tinubu ya aika sojoji su je Kano su nada Sarki. Bayan da majalisar jihar Kano ta rushe duka sabbin masarautun da tsohon gwamnan jihar, Umar Ganduje ya kirkiro, an mayar da tsohon sarki, Muhammad Sanusi akan kujerar sarautar Kano inda aka tsige Aminu Ado Bayero. Saidai Aminu Ado Bayero bisa rakiyar sojoji wadanda ake kyautata zaton Gwamnatin tarayya ce ta bashi su ya koma Kano inda ya yada zango a karamar fadar sarki dake Nasara. Shi kuma sabon sarki, Muhammad Sanusi II yana can fada yana karbar mubaya'a daga hakimai da sauran mutanen gari. An dai zargi me baiwa shugaban kasa shawara, Nuhu Ribadu da hannu a...