Saturday, December 14
Shadow

Kasuwanci

Labari me Dadi: Ji dalilin da zai sa Farashin Litar man fetur ya dawo Naira 300

Labari me Dadi: Ji dalilin da zai sa Farashin Litar man fetur ya dawo Naira 300

Kasuwanci
Rahotanni sun bayyana cewa kananan matatun man fetur na cikin gida ka iya karya farashin man fetur. Ana sa ran idan matatar man fetur ta Dangote da sauran matatun man fetur kanana suka fara aiki hakan zai sa farashin man fetur din ya karyo kasa. Saidai masana sunce idan ana son hakan ya tabbata watau farashin litar man fetur din ya dawo Naira 300 sai gwamnati ta tabbatar da ana baiwa matatun man na cikin gida isashshen danyen man fetur. A baya dai mun ji yanda Aliko Dangote ya koka da cewa, matatar mansa bata iya sayen danyen man Najeriya saboda kamfanonin dake hako man a cikin gida sun fi son su kai kasashen waje su sayar da danyen man fetur din.
Tapswap, Notcoin: Hatsarin shafukan kirifto da ‘yan Najeriya suka ruɗu da su

Tapswap, Notcoin: Hatsarin shafukan kirifto da ‘yan Najeriya suka ruɗu da su

Kasuwanci
Tun bayan fashewar Notcoins, matasa a Najeriya suka mayar da hankalai wajen yin mainin, domin tara maki ko 'points' a cikin manhajojin da suke amfani da su a wayoyinsu. Daga lokacin ne kuma harkar kirifto ke ƙara samun karɓuwa a Najeriya, inda a kowace rana ake samun ƙaruwar ɓullar sabbin shafukan mainin da ke alƙawarta samar wa mutane kuɗi. Masu amfani da shafukan ko manhajojin kan yi ta taɓa sikirin ɗin wayarsu domin samun wani maki da ake kira 'points', wanda za a iya canjawa zuwa kuɗi ''idan ta fashe''. A yanzu akwai sabbin manhajojin waya da dama da ake amfani da su domin samun kuɗin. Fitattu daga ciki sun haɗa da Notcoins da Tapswap da Hamstar Kombat da Poppo da sauransu. Yayin da wasu mutane ke darawa saboda kuɗin da suka ce sun samu sakamakon fashewar Notcoins, wasu ...

Ana kara mafi karancin Albashi zuwa Naira dubu dari da biyar(105,000) zan mayar da crate din kwaina Naira dubu goma(10,000)>>Inji Wannan me kiwon kajin

Kasuwanci
Wani me kiwon kaji ya bayyana cewa, Ana kara mafi karancin Albashi zuwa Naira Dubu dari da biyar(105,000) shima zai mayar da crate din kwansa Naira Dubu goma(10,000). Ya bayyana hakane a shafinsa na Twitter. https://twitter.com/BashorunGa_/status/1798770654571086102?t=m-LuPzJhHyNp7Q9xbyI_mA&s=19 Saidai da yawa sun masa chaa inda suke cewa bai kyauta ba. Saidai ya bayyana musu shima ma'aikacin gwammatine amma a gyara kasa yanda farashin kayan masarufi zai yi sauki, yafi a kara albashi.
Ina ake buga kudin nigeria

Ina ake buga kudin nigeria

Kasuwanci, Tarihi
Kanfanin Nigerian Security Printing and Minting (NSPM) ne ke buga kudin Najeriya. Kuma kamfanin na zaunene a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. A baya dai akan kai Kwangilar buga kudin zuwa kasashen waje amma a zamanin Mulkin Shugaba Buhari, an buga kudin na Naira a Najeriya. Saidai a duk sanda aka buga sabbin kudi, 'yan Najeriya kan yaba inda wasu ke kalubalantarsu, musamman ma dai ta bangaren ingancin Kudin.
Kanfanonin dake hako danyen man fetur a Najeriya sun ki sayar min dashi, sun kwammace su kaishi kasashen waje>>Dangote

Kanfanonin dake hako danyen man fetur a Najeriya sun ki sayar min dashi, sun kwammace su kaishi kasashen waje>>Dangote

Kasuwanci
Babban Attajirin Afrika, Aliko Dangote ya bayyana cewa, kamfanonin dake hako man fetur a Najeriya basa son sayar masa da danyen man fetur din. Ya bayyana hakane a hirar da gidan talabijin na CNN suka yi dashi inda yace kamfanonin sun saba da kai man fetur kasashen waje suna samun kudi dan haka sun ki sayar masa da danyen man. Yace da za'a sayar masa da danyen man, babu bukatar a rika sayo tataccen man daga kasashen turawa. Yace amma 'yan kasuwa dake shigo da man fetur din daga kasashen waje basa son hakan dan kuwa zasu rasa aiki. Saidai gwamnatin Najeriya ta bakin hukumar dake kula da harkar man fetur din, NUPRC, ta bayyana cewa zasu shiga tsakanin Dangote da kamfanonin dake hako man fetur din. Wakilin hukumar, Olaide Shonola ne ya bayyana haka a hirar da jaridar Punch ta yi...
Zan samu ribar Dala Biliyan $30 a karshen shekarar 2024>>Dangote

Zan samu ribar Dala Biliyan $30 a karshen shekarar 2024>>Dangote

Kasuwanci
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa nan da karshen shekarar 2024 zai samu ribar zunzurutun kudi har Dala Biliyan $30. Dangote ya bayyana hakane a hirar da CNN ta yi dashi. Ya bayyana cewa, hakan zai sa kamfaninsa ya shiga sanun kamfanoni 120 mafiya karfi a Duniya. Dangote dai a yanzu yana da mamatar man fetur wadda take daya daga cikin matatun man da ke da girma a Duniya.
Abin damuwane matuka yanda farashin Tumatir ya tashi daga Naira dubu arba’in(40,000) zuwa Naira dubu dari da hamsin(150,000) duk kwando daya>>Gwamnatin Tarayya

Abin damuwane matuka yanda farashin Tumatir ya tashi daga Naira dubu arba’in(40,000) zuwa Naira dubu dari da hamsin(150,000) duk kwando daya>>Gwamnatin Tarayya

Kasuwanci
Majalisar tattalin arzikin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana damuwa kan yanda farashin tumatur yayi tashin gwauron zabi. Ta bayyana hakane yayin da farashin tumatur din ya tashi daga Naira dubu arba'in(40,000) zuwa Naira dubu dari da hamsin (150,000). Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. Yace hauhawar farashin kayan masarufi na kara jefa mutane cikin wahala.