Friday, December 13
Shadow

Haihuwa

Alamomin nakuda

Haihuwa, Nakuda
Akwai alamomin nakuda da yawa, ga wasu daga cikinsu kamar haka: Jin matsewa a gabanki, zai rika matsewa yana budewa. Zaki rika jin shi kamar lokacin da kike jinin al'ada. Yayin da ruwa me kauri ya zubo daga gabanki. Ciwon baya. Jin kamar zaki yi kashi wanda hakan yana faruwane saboda yanda kan danki ke shirin fitowa waje. Da kin fara jin wannan alamomi to a garzaya a tafi Asibiti ko a kira ungozoma. Sauran Alamomin sun hada da zubar da jini. Abin cikinki ya daina motsi sosai.

Ya ake gane cikin mace

Haihuwa, Laulayin ciki
Idan ciki ya kai sati 20, gwajin Ultrasound yakan iya nuna cikin macene ake dauke dashi ko Namiji. Hakanan akwai gwajin Amniocentesis da shima ake yi wanda ke nuna jinsin jaririn da ake dauke dashi. Bayannan akwai alamu na gargajiya da ake amfani dasu wajan ganewa ko hasashen cikin mace. Ciki Yayi sama: Wasu na cewa idan ciki yayi sama sosai, to wannan alamace dake nuna cewa diya macece za'a haifa. Girman Nono: Hakanan akwai bayanan dake cewa idan nonon mace na hagu yafi na dama girma shima alamace dake nuna mace za'a haifa ba Namiji ba. Ciwon Safe: Ciwon safe na daya daga cikin dalilan da ake alakanta cikin diya mace dashi inda me ciki zata rika jin kamar zata yi amai, kasala da sauransu. Kalar Fitsari: Hakanan akwai bayanan dake nuna cewa kalar fitsarin mace ya zama kal...

Basir ga mai ciki

Basir Mai Tsiro, Haihuwa
Basir ga mata masu ciki ba sabon abu bane, wani bincike ya gano cewa,duk cikin mata masu ciki 3 ana samun macen dake da basur 1. Mata masu ciki na fama da basir saboda yanda jikinsu ke budewa dalilin daukar ciki da nauyin dan suke dauke dashi. Yawanci basir din mata masu ciki yana farawa ne a yayin da cikin ya fara nauyi,watau daga wata na 3 zuwa sama. Masana kiwon lafiya sun bayar da shawarar cewa,idan a baya kin taba cin basir yayin da kike da ciki,yana da kyau ki nemi shawarar likita a yayin da kika kara samun ciki. Maganin basir ga mai juna biyu Ga hanyoyin magance basir ga mai juna biyu kamar haka: A canja tsarin cin abinci: Canja tsarin cin abinci ta yanda za'a rika cin abinci me dauke da fiber,watau dusa, da kuma abinci me ruwa-ruwa, da shan ruwa akai-akai zasu tai...

Maganin rage zafin nakuda

Haihuwa
Radadin nakuda na daya daga cikin manyan abubuwan dake kayar da gaban mata wanda ke sa su rika neman abinda zai kawo musu saukinsa. A wannan rubutu, zamu kawo muku magunguna na gargajiya wanda likitoci suka tabbatar suna aiki wajan rage zafin Nakuda. Shan Zuma Ta tabbata likitoci sun ce mace me ciki dake shan zuma na samun saukin Nakuda sosai ba kadan ba. Hakanan a lokacin nakudar ana iya baiwa mace me ciki zuma ta rika sha, shima yana taimakawa sosai wajen rage radadin Nakudar. Amfani da Zuma da Dabino Hakanan kuma Hada zuma da Dabino a yi blendinsu a sha, shima yana taimakawa rage zafin nakuda da sawa ta a samu nakuda wadda bata da tsawo, watau a haihu da wuri. Wannan sahihin maganin nakuda ne dan an kwada akan mata da yawa wanda aka yi bincike dasu kuma yayi aiki. Amfa...

Kumburin kafa ga mai ciki

Haihuwa, Laulayin ciki
Mai ciki zata yi fama da kumburin kafa, musamman idan cikin ya fara girma. Hakan na faruwane saboda nauyin abinda ke cikinta. Hakan nasa jini ya rage gudana a kafarki, Musamman idan ana yanayim zafi ko kuma kin dade a tsaye. Bayan girman da abinda ke cikinki yake yi, a yayin da kike da ciki, yawan ruwan dake jikinki yana karuwa. Hakan kuma nasa ciwon kafa. Kafa da gwiwoyinki da tafin kafa da yatsu duk zasu iya kumbura. Yayin da cikinki ke kara girma, kumburin shima zai rika karuwa a hankali. Saidai wannan kumburi idan dai ba ya wuce lissafi ba, bashi da cutarwa ga Mahaifiya ko abinda ke cikinta. Alamomin dake nuna kumburin me ciki me cutarwane kuma yana bukatar kukawar likita Idan lokaci guda kumburin ya karu a fuska, hannu da tafin kafa. Idan ciwon kai me tsa...

Alamomin cikin wata tara

Duk Labarai, Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 9, abinda ke cikinki na da cikakkiyar halittar Idanu kuma za'a iya cewa ya cika mutum. A wata 9, abinda ke cikinki ya kai tsawon 12 inches ko ace 30 cm Idanun sun yi kwari sosai zasu iya kallon komai. Gashin da ya lullube jikin jaririn kusan za'a iya cewa ya gama zubewa. Hakanan fatar jikin jaririn ta yi kwari. Yayin da cikin ki ya kai wata tara, zai ci gaba da yi miki nauyi. Alamomin daukar ciki, irin su nankarwa, Rashin lafiyar safe, Kasala, kasa rike fitsari, da sauransu zasu ci gaba har zuwa a haihu. Abinda ke cikinki zai iya yowa kasa, wanda hakan zai rage miki wahalar yin kashi da zafin kirji ko zuciya. Saidai cikin wasu matan bai yo kasa har sai nakuda ta tashi.

Alamomin cikin wata takwas

Duk Labarai, Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 8, abinda ke cikinki ya kai tsawon 11 inches. A daidai lokacinne wani gashi me laushi dake lullube da abinda ke cikinki zai fara zubewa. Idan namiji ne, a wannan lokacinne marainansa zasu zazzago kasa. A wannan watanne zaki rika jin gajiya, sannan zaki rika nishi da kyar. Jijiyoyi zasu iya fitowa rado-rado musamman a kafarki. Zaki iya samun nankarwa. Zafin kirji ko zafin zuciya na iya ci gaba, hakanan zaki iya ci gaba da fama da wahala wajan yin kashi. Fitsari zai iya zubowa yayin da kika zo yin atishawa ko kuma kike dariya. Wadannan abubuwanne zaki yi fama dasu yayin da cikinki ya kai watanni 8.

Alamomin cikin wata biyu

Haihuwa, Laulayin ciki
A sati na 5 zuwa 6, abinda ke cikinki zai fara canjawa inda zai shiga matakin Embryo wanda daga wannan mataki ne za'a fara halitta. Zai dunkule a waje daya wanda zai zama kamar zuciya amma bai gama zama zuciyar ba. Idan aka duba a ma'aunin Ultrasound za'a iya jin yana motsi kamar zuciya. Alamun fitowar hannuwa da kafafu zai bayyana. Halittar da Kwakwalwa, jijiyoyi da sauran manyan sassan jiki zasu fita daga ciki zata bayyana. Alamar bindi zata bayyana. Ya yin da cikin ya cika sati 8, watau wata biyu daidai, zuciya zata bayyana Yatsun hannu da na kafa zasu fara bayyana. Ido, kunne, marfin ido ko fatar ido zasu fara bayyana. Da leben sama. A wata na biyu, har yanzu alamomin daukar ciki suna nan tare dake kamar su zafin nono, kasala, yawan fitsari, zafin kirji ko zuciy...

Alamomin cikin wata bakwai

Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 7, zaki iya fuskantar matsala saboda nauyin abinda ke cikinki. Gwiwoyi da kafafuwanki zasu iya kumbura. A wannan lokaci ne ya kamata ki samu ilimi kan haihuwa saboda kina kusa da haihuwar. Canji a jikin uwa bayan da ciki ya kai wata bakwai: Zaki iya samun matsalar rashin bacci. Zaki iya samun matsalar zubewar gashi wanda bayan kin haihu zai dawo. Zaki iya ganin karuwar gashi a fuska, gabanki, hamata, kafa da baya Faratan ki zasu rika girma sosai. A yayin da cikinki ya kai watanni 7 da haihuwa, zaki fuskanci fargaba saboda kin kusa haihuwa, zaki rika tunanin nakuda da rainon yaron. Halartar wajan bitar abubuwan da zaki yi nan gaba wajan haihuwa da bayan haihuwa zai taimaka sosai. Canje-Canjen da ake samu a jikin jariri yayin d...

Cikin wata hudu

Haihuwa, Lauyayin ciki, Nakuda
Bayan cikinki ya kai wata 4, ga abubuwan dake faruwa: Dan dake cikinki ya kai girman inchi 3 ko ace 8 cm. Za'a iya gane wane jinsi ne abinda ke cikinki saboda za'a iya ganin al'aurarsa a na'urar gwaji ta Ultrasound. Gashin kan abinda ke cikinki ya fara fitowa. An halicci saman baki ko lebe. Da yawa daga cikin Alamomin farko da kika fara ji na daukar ciki zasu daina damunki bayan da cikinki ya kai watanni 4. Saidai matsalolin rashin narkewar abinci zasu iya ci gaba da bayyana a jikinki, kamar wahala wajan yin kashi, zafin kirji ko zuciya. Nononki zai kara girma, zai rika zafi sannan kan nononki zai kara yin baki. Zaki iya samun matsalar numfashi sama-sama ko kuma yinshi da sauri. Dasashin bakinki zai iya yin jini, zaki iya yin habo, watau zubar da jini ta hanci, ...