Cikin wata biyar
Duk da yake cewa kowace mace da irin yanda ta ke daukar cikinta amma a wata 5 da daukar ciki, za'a ga girman cikinki ya bayyana.
Jikinki zai fara canjawa yana daidaituwa da yanda cikinki ke kara girma.
Ga wasu alamu da ke nuna cewa cikinki ya kai wata 5:
Kafafunki zasu Kumbura: saboda nauyin da kika kara saboda cikin dake jikinki, kafafunki zasu iya kumbura, kwanciya a daga kafa sama yana taimakawa wajan magance wannan matsala.
Ciwon kwankwaso: Saboda yanda cikinki ke fitowa, bayanki zai rika shigewa ciki wanda hakan zai iya kawo miko ciwon kwankwaso.
Juwa: A yayin da jaririnki ya ke girma, yawan jinin dake gudana musamman zuwa kanki zai iya raguwa wanda zai sa ki ji juwa.
Mura: Zaki iya fuskantar Mura, hancinki ya toshe ko kuma yayi ta yoyo, kai yana ma iya fitar da jini...