Monday, December 16
Shadow

Kiwon Lafiya

Meke kawo ruwan nono ga budurwa

Nono
Yawancin abinda ke kawo ruwan nono shine haihuwa. Bayan mace ta haihu, ruwan nononta na zuwa sosai. Bayan haihuwa akwai wasu abubuwan na daban da kan iya kawowa budurwa ruwan nono: Yawan tabawa da matsa nonon budurwa yana iya sawa ya kawo ruwa. Shan wani magani da jikin budurwar be yi amanna dashi ba yana iya sata reaction ruwan nononta ya kawo. A wasu lokutan ma haka kawai babu dalili, nonon budurwa zai iya kawo ruwa. Yanda ake tsayar da zubar ruwan nono Zubar nono na raguwa da kanta daga lokaci zuwa lokaci. Amma akwai abubuwan da za'a iyayi dan magance matsalar. A daina matsa nonon. Wasu lokutan ana gwada daure nonon da tsumma me kyau.

Kaikayin nono ga budurwa: Meke kawo kaikayin nono ga budurwa

Kiwon Lafiya
Kaikayin nono ga budurwa na iya zuwa saboda wani abu data ci ko kuma haka kawai, ko saboda jinin al'ada, ko bushewar fatar kan nonon da sauransu. Ga abubuwa 11 dake kawo kaikayin nono ga budurwa: Tana iya yiyuwa wajan yayi bori ne ko wani kurjine ya fito akan nonon. Idan kika yi amfani da sabulun da be karbeki ba ko kuma jikinki baya so, zai iya saka kaikai a jiki hadda ma kan nono. Saka rigar mama wadda ta matse ki na iya sawa kan nonon ki yin kaikai. Idan hakane, ki saka rigar mama wadda bata matseki sosai ba. Tana iya yiyuwa kin yi zufa kika barta ta bushe a jikinki, hakan na iya kawo kaikan kan nono. Lokacin Al'ada nasa kan nonon mace ya rika kaikai. Akwai kuma ciwon kansar mama wanda idan kai kayin yayi yawa ya kamata ki je Asibiti.

Sau nawa ake jima’i: Sau nawa ya kamata ayi jima’i

Duk Labarai, Jima'i, Kiwon Lafiya
Wani bincike ya nuna cewa yin jima'i sau daya a sati yana baiwa ma'aurata natsuwa. Hakanan kuma wasu masana halittar dan adam sun bayyana cewa, yin jima'i kasa da sau 10 a shekara na nufin cewa ma'aurata na cikin auren da babu jima'i, watau hakan yayi kadan matuka. Saidai kuma wani bincike ya nuna cewa, idan aka yi sabon aure, yayin da suke amarya da ango, ma'aurata kan yi jima'i kusan har sau 3 ko 4 a rana. Hakanan, idan ma'aurata na son samun haihuwa, shima sukan yi jima'i da yawa da tunanin ko ciki zai shiga. Magana mafi inganci itace, babu wata matsala idan mutum na yin jima'i a kullun. Masana sunce, Jima'i na saka mutum farin ciki nan take kuma yana yayewa mutum damuwa. Jima'i yakan iya zama yana da illa ne kawai idan: Ya zamana ya hana ka yin ayyukan ci gaban ra...

Lokacin da mace tafi daukan ciki

Kiwon Lafiya
Macw tafi daukan ciki lokacin tana Ovulation, watau bayan ta gama haila a lokacin da take ganin wani farin ruwa me kamar kwai. Wannan ruwa shine yake taimakawa maniyyin namiji ya shiga mahaifa ya zauna har ya hadu da kwan mace ya zama mutum. Likitoci sun ce a wannan lokaci ne aka fi samun ciki, kuma suna bada shawarar ayi jima'i a wannan lokaci. Saidai kuma sunce yawan yin jima'in baya kawo saurin daukar ciki.

Hanyoyin samun ciki da wuri

Kiwon Lafiya
Ga hanyoyi 7 da masana kimiyya suka tabbatar da idan aka bisu ana samun ciki da wuri: Masana sunce Idan ana son samun ciki da wuri to a yi amfani da folic Acid kamin fara jima'i. Ana samun sunadarin Folic Acid a Ganye irin su latas, da Kwai, wake, Ayaba, Lemu, da gyada. Kuma ana samun maganin Folic Acid wanda za'a iya tambayar likita idan ba'a samu damar cin wadancan abubuwan ba. Ciki na shiga da wuri idan mace na Ovulatin. Zaki gane idan kina Ovulation idan kika ga wani farin ruwa kamar na danyen kwai yana fitowa daga gabanki. Wannan ruwan yana taimakawa maniyyi ya kai ga mahaifa ya zauna a samu ciki. A daidai wannan lokaci idan aka yi jima'i dake akwai kyakkyawan zaton mace zata dauki ciki. Babu wata kalar kwanciyar da masana suka ce tana saurin sa a dauki ciki. Ki c...
Kalli Hoto: Sabuwar cuta dake yaduwa ta hanyar Jima’i ta bayyana

Kalli Hoto: Sabuwar cuta dake yaduwa ta hanyar Jima’i ta bayyana

Kiwon Lafiya
Wata cuta da aka kira da Ring worms dake yaduwa ta hanyar Jima'i ta bayyana. Cutar dai wadda irintace a karin farko da aka gani a jikin dan adam ta bayyana ne a jikin wani dan kasar Amurka. Mutumin dai dan Luwadi ne wanda kuma yaje kasashe daban-daban yayi lalata da maza masu yawa. Bayan da ya koma kasarsa ta Amurka ne sai aka ganshi da wannan cuta. Saidai masana kimiyyar lafiya sun ce kada mutane su tayar da hankali dan cutar bata kai matakin barazana ga sauran al'umma ba. Ko da dai cutar Kanjamau akwai wasu majiyoyi dake cewa daga wajan 'yan Luwadi aka fara samota, hakanan ta tabbata cewa masu Luwadi sun fi saurin kamuwa da cutar.
Idan mutum na son cin abinci me rai da lafiya sai ya kashe Naira 1,050 a kowace rana>>Inji Gwamnatin Tarayya

Idan mutum na son cin abinci me rai da lafiya sai ya kashe Naira 1,050 a kowace rana>>Inji Gwamnatin Tarayya

Kiwon Lafiya
Hukumar Kula da gididdiga ta kasa NBS ta bayyana cewa kudin da mutum zai kashe ya ci abinci me gina jiki a Najeriya ya kai Naira 1,050 a kullun. NBS ta bayyana hakane a wani rahoto data fitar ranar Laraba akan farashin abinci me gina jiki. Tace a watan Maris, Naira 982 ake kashewa wajan cin abinci me gina jiki yayin da a watan Afrilu ya karu zuwa Naira 1,050. NBS tace wannan farashin abincine da bashi da tsada wanda kuma ake samunsa a gida Najeriya amma kuma yana da duk sinadaran da Duniya ta yadda dasu na gina jiki. Yayin da hukumar ta fitar da kudin da ake kashewa wajan cin abinci me gina jiki a kowane bangare na Najeriya, tace bangaren Arewa maso yamma nan ne ake kashe kudi mafiya karanci wanda suka kai Naira 781 wajan cin abinci me gina jiki a kullun. Jihohin Kudu maso y...
Karanta Jadawalin yawan likitocin da kowace jiha ke dasu a fadin Najeriya

Karanta Jadawalin yawan likitocin da kowace jiha ke dasu a fadin Najeriya

Kiwon Lafiya
Wannan jadawalin yawan likitocin da kowace jiha ke dasu ne a Fadin Najeriya: Lagos: 7,385 FCT: 4,453 Rivers: 2,194 Enugu: 2,070 Oyo: 1,996 Edo: 1,777 Kaduna: 1,524 Anambra: 1,518 Ogun: 1,511 Kano: 1,477 Delta: 1,456 Osun: 1,294 Plateau: 1,200 Imo: 1,110 Kwara: 1,016 Ebonyi: 899 Akwa Ibom: 888 Abia: 829 Cross River: 826 Ondo: 743 Borno: 736 Bayelsa: 727 Ekiti: 695 Benue: 621 Sokoto: 602 Katsina: 562 Nassarawa: 552 Niger: 494 Gombe: 485 Bauchi: 443 Kogi: 418 Adamawa: 280 Yobe: 275 Kebbi: 273 Zamfara: 267 Jigawa: 255 Taraba: 201

Meke kawo ciwon mara lokacin al ada

Magunguna, Matsalolin Mara
WASU ABABE DAGA CIKIN DALILAN DAKE HAIFAR DA CIWON MARA LOKACIN AL'ADA. Da dama dai a bangaren lafiya abunda muke dauka ba kome ba zai iya haifar mana da damuwa ko kara tsananta wani hali ko yanayin da muke ciki. A Bangare al'ada da dama mata kan hadu ko ji alamun ciwon mara lokacin da suke al'ada, ko kafin su fara ko bayan angama da wasu lokuta. TO GA WASU RIKUNNEN ABINCI WADAN DA KE KARA MATSALAR CIWON MARA LOKACIN AL'ADAR Matukar mace zata rika anfani dasu to akwai yiyuwar karuwar matsalar. 1. Chacolate2. Sugar3. Coffee4. Dairy foods5. Processed food6. Fatty food7. Salty food Matukar mace zata rika anfani da kowane nau'in abinci mai dauke da sanadaran daidaikun wadancen kayan abinci matsalar primary amenorrhoea zata iya karuwa. CONTRACTIONS Na mahaifa na daga cikin dal...

Yadda ake gwajin ciki da gishiri

Gwajin Ciki, Magunguna
Ana yin gwajin ciki da gishiri a gida dan gane ko mace na da ciki ko bata dashi. Yanda ake yinshi shine: Ana samun kofi ko mazubi a yi fitsari a ciki sai a zuba gishiri a ciki kamar chokali 2 zuwa 3. Sai a barshi zuwa minti 1 ko 5. Idan yayi ruwan madara ko yayi gudaji, to alamar mace na da ciki kenan. Idan kuma ya tsaya a yanda yake ba tare da ya canja ba to baki da ciki. Saidai shi wannan gwaji na gishiri bashi da inganci a wajen masana kiwon lafiya kuma babu wata hujja ta ilimi data tabbatar da sahihancinsa. Hanya mafi inganci da ake yin gwajin ciki itace ta hanyar zuwa Asibiti a gwada mace ko kuma amfani da tsinken gwaji wanda ake cewa pt strip test. Mun yi rubutu kan yanda ake yin wannan gwaji: Yadda ake amfani da tsinken gwajin ciki