Maganin yawan fitsari
Yawan fitsari matsala ce dake sa mutum ya rika yin fitsari fiye da kima, idan ya zamana mutum na yin fitsari fiye da sau 8 a rana, za'a iya cewa yana yawan fitsari.
Wannan matsala zata iya faruwa ga kowa amma tafi yawa a tsakanin mutanen da suka zarta shekaru 70 a Duniya, da mata masu ciki, ko bayan fara shan wani magani, ko kuma wani me wata cuta ta musamman.
Yawan Fitsari na iya zama alamar daukar ciki ga mace, sannan yana iya zama alamar ciwon sugar wanda ake cewa diabetes ko ciwon mafitsara, da sauransu.
Masana kiwon lafiya sunce ba matsala bace idan mutum ya tashi da dare yayi fitsari, sun ce idan mutum ya kai shekaru 40 zuwa 50, to zai iya fuskantar tashi cikin dare yayi fitsari sau daya. Idan kuma mutum yana tsamanin shekaru 60 zuwa 70, zai iya rika tashi cikin dare yana yi...