Me ke janyo ciwon baya: Maganin ciwon baya mai tsanani
Ciwon baya na iya samun babba ko yaro, sannan yana iya samuwa a kasan baya, wajan kugu, ko kuma a saman baya.
Akwai dalilai da dama dake kawo ciwon baya wadanda zamu zayyano a kasa:
Jin ciwo na zahiri
Daga wani Abu ba yanda ya kamata ba.
Daga wani abu me nauyi sosai.
Motsi ba daidai ba.
Ciwon gabobi wanda tsuwa ke kawowa.
Tari ko Atishawa.
Yin mika ba daidai ba.
Dukawa ta tsawon lokaci.
Turawa, jaa, ko daukar wani abu.
Zama ko tsayuwa na tsawon lokaci.
Yin tuki na tsawon lokaci.
Kwanciya akan katifar da bata dace da jikinka ba.
Akwai ciwon dajin dake kawo ciwon baya.
Su wanene ciwon baya yafi kamawa?
Akwai mutanen da yanayin da suke ciki ko kuma irin abubuwan da suke yi ke sa sufi zama cikin hadarin kamuwa da ciwon baya.
Irin wadannan mu...