Wednesday, October 9
Shadow

Maganin ciwon ido kowane iri

Maganin ciwon ido ya danganta da dalilin samuwar ciwon idon.

Idan ciwon idon ya fara ne dalilin wani abu da aka ci ko aka shafa, a kyaleshi zai warke da kansa.

Akwai magungunan digawa, dana shafawa dama na sha wanda ake amfani dasu kuma yawanci cikin awanni 24 suke warkar da ciwon ido.

Amma ga magunguna kamar haka da za’a iya amfani dasu:

Ana iya amfani da tsumma me dumi ko kuma me sanyi wanda ba mai cutarwa ba kuma a samu tsumman me kyau, wankakke a dora akan idon.

Ana kuma iya amfani da maganin digawa.

Ana iya murza idon amma ba sosai ba.

Karanta Wannan  Maganin matsi ciki da waje

Ana kuma iya saka jakar Grean Tea a cikin Firjin idan ta yi sanyi a dora akan idon.

Shima Ruwan Gishiri ana amfani dashi wajan magance irin wadannan matsalolin.

Wane Lokaci ne ya kamata a ga Likita?

Idan ciwon idon be warke da kansa ba ko kuma an yi amfani da dabarbarun sama amma bai warke ba, bayan kwana biyu to a tuntubi Likita.

Hakanan idan aka ji zafin ciwon na karuwa, Gani yana dusashewa, to a gaggauta zuwa ganin Likita.

Mun tattaro bayanai daga kafofi wanda likitoci suka aminta dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *