Saturday, December 14
Shadow

Soyayya

Maganin farin jinin samari

Soyayya
Babban maganin farin jinin samari shine yin Addu'a. Yin addu'a musamman a karshen dare ki gayawa Allah abinda kike so zai sa ki samu farin jinin samari da yardar Allah. Abubuwan da zaki tsare sun hada da: Ki zama me tsafta. Kamun kai. Iya magana. Kar ki zama me rashin kunya. Iya kwalliya, saidai hakan ba yana nufin nuna tsiraicin ki ba. Yawanci zaki ga farin jini daga Allah ne, amma babu abinda ya gagari Allah, idan kika dukufa wajan addu'a, zaki samu abinda kike so.

Kuka a daren farko

Auratayya, Soyayya
Mafi yawanci bisa al'ada amare na kuka a daren farko da suka shiga dakin mijinsu bayan an daura aure. Saidai basu kadai ne ke wannan kukan ba. Da yawa ciki hadda iyayen amarya, uba da uwa dukan akan samu wadanda ke yin wannan kuka. Yawanci iyaye kan yi kukane bayan an daura aure a lokacin da ake tafiya da amarya zuwa gidan mijinta tana musu bankwana ko kuma suka gama yi mata nasiha. A daidai wannan lokaci hawaye yakan kwacewa iyayen amarya. Saidai wasu ba'a ganin nasu, suna yin na zuci ne kawai, ko kuma sai dare yayi sun ga gurbin diyarsu anan ne hawaye ko kukan zuci zasu fara bayyana a fuskar iyaye. Ita kuwa amarya a mafi yawan lokuta tana fara kukanta ne a yayin da aka kamota za'a sakata cikin mota dan zuwa gidan miji daga gidansu. Za'a tafi da ita tana kuka har zuwa...

Addu’ar barka da safiya

Addu'a, Soyayya
Aminci da yarda ya k'ara tabbata ga mamallakinzuciyata,farin wata mai haskaka zuciyata,kaineka zamo farin cikin rayuwa,ina da tabbacin cewazuciyarka tana cike da so nada bege na acikin wannan sansanyar safiyarkamar yanda tawa ta kasance haka,zai zamaabin alfaharina cewa wannan sak'on nawa shineabu mafi soyuwa daya fara riskarka cikin wannanni'imtacciyar safiyar masoyina…Ina fatan ka tashi lafiya. Duk sha'aninka na rayuwa, kar ka cire Ubangiji ciki, kana buƙatar Allah a kowannen lokaci. A ruwaito daga Anas bin Malik (12AH - 93AH) cewa, Manzon Allah ﷺ ya yi Nana Fatima عليها السلام wasici da karanta wannan addu'ar safiya da maraice: "يا حي يا قيوم برحمتك أستغيث أصلح لي شأني كله ولا تكلني إلى نفسي طرفة عين" Ma'ana: "Ya Rayayye, Ya Mai tsayuwa da komai! Da rahamarKa nake neman taim...

Saurayina ya yaudareni

Soyayya
Akwai zafi da daci da bakin ciki da dana sani idan saurayi ya yaudari budurwarsa. Da farko zaki rika jin me zaki yi dan ki rikeshi kada ya barki, watakila ki rokeshi, watakila ki rika addu'a, zaki iya yin kuka a gabanshi ko ke kadai a daki. Wannan yanayi akwai radadi da zafi. Saidai idan zaki iya, kada ki yawaita magana da kowa idan kika shiga wannan yanayi, dan kuwa a wannan yanayi duk wanda kike magana dashi zaki iya gaya masa sirrikanki wanda bai kamata wani ya sani ba. Sai daga baya ki rika dana sani. A irin wannan yanayi zaki ji jikinki yayi sanyi, zaki ji kamar baki da amfani, zaki ji kin rude, zama ki iya jin dama ki mutu. Tambaya ta farko shine, Saurayinki da ya rabu dake ya taba yin zina dake? Tambaya ta biyu ya miki ciki? Tambaya ta uku, yana da hotunanki na ...

Nasiha zuwa ga budurwa

Ilimi, Soyayya
'Yan mata adon gari, kin taso kin fara kwalliya kina son ki yi saurayi, ko kumama kin taba yi, ga wasu nasihohi da zasu amfaneki idan kika yi Amfani dasu Insha Allah: Babu namiji dake sonki fiye da mahaifinki, Mahaifinki ya fi kowa sonki a Duniya, Dan haka kada ki biyewa rudin saurayi yasa ki ki aikata abinda ba daidai ba saboda kina tsoron karki saba masa, idan ya rabu dake insha Allahu zaki hadu da wani me sonki. Mahaifiyarki ta fi kowace mace sonki a Duniya: Hakanan kada rudin soyayya yasa ki biyewa saurayi ku aikata abinda ba daidai ba ko yasa ki sabawa Allah ko Iyayenki saboda tsoron karki rabu dashi, ki mai Nasiha, idan yaki, kada ki biye masa, ga soyayya ta gaskiya nan a gurin iyayenki mahaifi da mahaifiya. Ka da ki yadda da kalmar Bazan barki ba ta saurayi: Duk da ba duka...

Nasiha ga masoyiyata

Soyayya
Masoyiyata ki rike karatu na Boko dana Islamiyya, Allah ya sanya miki Albarka a rayuwa. Masoyiyata ki yiwa iyayenki biyayya da neman Albarkarsu, ki gujewa abinda zai bata musu rai. Masoyiyata ki rika Istigfari dan kullun cikin sabo muke, kuma ki rika salati ga Annabi dan neman hasken rayuwa da ceto a Duniya da Lahira. Masoyiyata ki rika karatun Qur'ani dan fita daga kunci da neman biyan bukata da farin cikin Duniya da lahira. Masoyiyata ke kyakkyawace, maza da yawa, masu niyya me kyau da masu mummunar niyya zasu ta kawo miki hari, kada ki yadda da duk wani wanda burinshi kawai ya taba jikinki. Masoyiyata, ki kula, kada ki bi rudin zamani waja bayyana surar jikinki, Allah ya miki daraja da kima kada ki zubar da ita a titi wajan yin shigar banza wadda zata jawo miki shedanun ...

Sakon fatan nasara ga masoyi

Soyayya
Masoyina ina maka fatan Allah ya kareka. Addu'a nake maka kullun Rabbana ya hore. Allah yasa ka fi haka. Masoyina Allah ya kawo budin kasuwa ya daukaka ka akan sa'anninka. Ina maka fatan kamar yanda kake neman Arziki ta hanyar halaliya, Allah ya Azurtaka ta hanyar halaliya. Ina Addu'ar Allah ya makantar da kai daga ganin haram, ya bude idanunka wajan ganin halal, Allah ya hana bakinka cin haram, ya bude maka shi wajan cin halal, Allah ya daure hannuwanka kada su kai ga Haram, Ya sakesu su yi walwala wajan yakin neman Halal. Masoyina kullun ina alfahari da kai kan yanda kake jajircewa wajan neman na kanka, ina fatan Allah ya wadatar dakai. Makiyanka sai sun yi kunci saboda nasarar da zaka samu, mahassadanka sai ciwon zuciya ya kamasu saboda daukakar da zaka samu, sa'ann...

Sakon rashin lafiya ga masoya

Soyayya
Allah ya baki lafiya masoyiyata. Ina fatan wannan rashin lafiya ta zama kaffara ga zunubanki. Rashin lafiya ka iya zama Alheri ta hanyar kankare zunubai idan mutum ya dauka cewa kaddara ce daga mahalicci ba wanine ko rashin wayonsa ne ya dora masa ba, ina fatan kina da wannan yakini dan samun amfanin wannan dama. Cuta ba mutuwa bace masoyiyata ki koma ga Allah da neman gafarar zunubai. Kullun ina sakaki a addu'a Allah ya baki lafiya masoyiyata. Masoyiyata ki daure ki tashi, Dan amfanin kanki da sauran na kusa dake. Masoyiyata insha Allahu zaki warke, ki yi imani da Allah da kuma fatan cewa zai baki Lafiya. Masoyiyata ba zan iya jure rashinki ba, Insha Allahu kina daf da samun lafiya. Duk runtsi duk wuya ina tare dake, wannan rashin lafiya jarabawace wadda kuma zata ...

Addu’a ga masoyiyata

Addu'a, Soyayya
Ina fatan Allah ya haskaka rayuwarki. Fatana shine ki fi kowa a tsakanin sa'anninki. Allah yasa mu zama mata da miji. Allah yawa soyayyarmu Albarka ta yanda zamu yi aure mu haifi 'ya'ya masu Albarka. Ina fatan Allah ya kareki daga sharrin makiya, Mahassada da kambun baka, masoyiyata kada ki manta da karanta falaki da Nasi safe da yamma. Kina da kyau, dan haka nasan akwai mahassada da masu mugun baki, fatana shine Allah ya kareki daga dukkan sharrinsu. Kina da Basira, Fatana shine Allah ya kareki daga sharrin mahassada. Babyna ki kasance kullun cikin zikiri, zaki rabauta daga sharrin shedan la'ananne. Insha Allahu duk inda zaki shiga sai Allah ya hadaki da masoya na gaskiya. Babban burina shine inga Allah ya daukakaki a tsakanin sa'anninki. Masoyiyata Ki rike s...

Hirar soyayya

Kalaman Soyayya, Soyayya
Ga wasu misalan yadda hirar soyayya za ta kasance tsakanin masoya: Misalin Hirar Soyayya Domin Sanya Murmushi: Maigida (A): "Barka da safiya, kyakkyawar tauraruwa ta." Amarya (B): "Barka dai, masoyina. Yaya ka tashi?" A: "Na tashi lafiya, musamman yanzu da na ji muryarki. Ke fa?" B: "Na tashi lafiya, amma yanzu na fi jin daɗi da na yi magana da kai." A: "Ko kin san cewa murmushinki yana iya haskaka rana ta?" B: "Ka san dai kana sa ni jin kamar sarauniya a kowane lokaci, ko?" Misalin Hirar Soyayya Mai Tsawo: Maigida (A): "Kina tunanin abin da zan iya yi don na faranta miki?" Amarya (B): "Gaskiya ka riga ka yi komai. Amma ka san na fi son lokacin da muke tare, ko?" A: "Ni ma haka nake ji. Ina son lokacin da muke tar...