Friday, December 13
Shadow

Soyayya

Yanda mace zata yi kukan shagwaba

Soyayya
Macen da bata da shagwaba ta samu nakasu a wajan cikar dabi'arta. Ya kamata mace ta iya gwaba ma mijinta. Guraren da ya kamata mace ta yiwa mijinta shagwaba: Guraren da ya kamata mace tawa mijinta Shagwaba sun hada da Wajan rokon wani abu daga wajen mijinta. Wajan Hira ta soyayya, misali idan miji zai tafi wajan aiki ko kasuwa, ya kamata su rabu da matarsa tana mai shagwaba sosai. Hakanan wajan Kwanciya ma ya kamata mace ta rikawa namiji shawagaba sosai. Shagwaba daga kallo take farawa, irin kallon da zaki rikawa mijinki kadai ya isa ya tayar masa da hankali. Sannan sai magana a hankali da kuma uhum..uhum dinnan kin gane dai. Jikinki ma yana shawagaba, wajan juyashi da jiginawa mijinki duk abubuwan da suka dace duk dan ki jawo hankalinsa. Ya kamata mace ta iya na...

Addu’ar janyo hankalin saurayi

Soyayya
A sunnah ta ma'aiki, Sallallahu Alaihi Wasallam babu wata addu'a da aka ruwaito cewa itace ta janyo hankalin saurayi. Saidai zaki iya rokon Allah ya baki soyayyar wane, idan shine Alkhairi. Kuma mafi kyawun hanyar da ya kamata ki bi wajan yin wannan addu'a shine ta hanyar yin Istikhara. Jabir ibn ‘Abd-Allah(RA) ya ruwaito cewa, Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam yana koya mana neman zabin Allah(yin Istikhara) kamar a dukkan al'amuran mu, kamar yanda ake koya mana karatun Qur'ani. Yace duk wanda yake da wata damuwa akan wani abu da yake nema ko yake so to yayi raka'a biyu sai yace "Allahumma inni astakhiruka bi ‘ilmik, wa astaqdiruka bi qudratik, wa asaluka min fadlik al-azim. Fa innaka taqdiru wa la aqdir, wa ta’lamu wa la a’lam, wa anta ‘allamul-ghuyub. Allahumma in kunt...

Sunayen mata masu dadi

Kalaman Soyayya, Soyayya, Sunaye
SUNA YEN YARA MATA DA MA,ANRSUWARE SUNAN DA KAKE SHA,AWA KASAWADIYARKI/KI.-------------------1.Eeman (imani)2.Ameerah (gimbiya)3.Ihsan (kyautatawa)4.Intisar (Mai nasara)5.Husna (kyakyawa)6.Mufida (Me amfani)7.Amatullah (Baiwar Allah)8.Ahlam (Me kyawawan mafarkai)9.Saddiqa (Mai gaskiya)10.Sayyada (Shugaba)11.Khairat (Me alkhairi)12.Afaf (Kammamiya)13.Basmah (Murmushi)14.Nasreen (Wata fulawa mai kamahi a gidanaljannah)15.Salima (Mai aminci)16.Rauda (A cikin masjid nabawi)17.Samha (Mai kyau)18.Siyama (Mai azumi)19.Sawwama (Mai yawan azumi)10.Kawwama (Mai Sallar Dare)11.Nuriyyah (Haskakawa)12.Noor (Haske)13.Sabira (Mai hakuri)14.Meead (alkawari)15.Islam (Musulunci)16.Nawal (Kyauta)17.Afrah (Farin ciki)18.Mannal (Wadata)19.Faiza (babban rabo)20.Hannah (Mai tausayi)21.Sajeeda (Mai yawan sallah)2...

Yadda ake hirar soyayya a waya

Soyayya
Hmmm.... Lallai kina son ko kuma kana son ka iya hirar soyayya a waya ko? To bari dai in fara da cewa, a mafi yawancin lokuta ba a koyata, yanayinkane ke sa budurwa ta soka ko ta kika, ko kuma saurayi ya soki ko ya kiki. Idan budurwa na sonka, kusan duk abinda kayi daidai ne, hakanan shima saurayi idan yana sonki. Saidai akwai shawarwari da zan baku da zasu sa ku iya hirar soyayya ta waya. Yadda ake hirar soyayya a waya Da farko dai ya kasance kana yawaita kuranta budurwarka. Ka rika gaya mata irin kyan da take dashi, wane fim ne ake yayi a lokacin, wane labari me dadine ya faru a irin wannan yanayin, wane abune kake tunanin bata sani ba wanda kai ka sani da kuma kake tunanin zai birgeta? Idan zaka gaya mata magana, ka rika hada mata da misali na zahiri wanda ya far...

Alamomin cikakkiyar budurwa

Soyayya
A jiki ana gane alamomin cikakkiyar budurwa kamar haka: Nonuwanta zasu ciko Wata Kugunta zai kara girma Gashin gaba Gashin hamata Fuskarta zata rika sheki Muryarta zata kara zama siririya A halayya ana gane alamomin cikakkiyar budurwa kamar haka: Zata rage yawan magana Zata rika kula da kanta fiye da da Wata zata rika kebancewa ita kadai Zata san darajar kanta Zata so yin saurayi. Wadannan sune alamun cikakkiyar budurwa wanda ba lallai a samesu wajan yarinya ko kwaila ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa: A shafin twitter zaku same mu a @hutudole A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Gajerun sakonnin soyayya

Kalaman Soyayya, Soyayya
Ga Gajerun sakonnin soyayya masu rasha jiki kamar haka: Duk yadda zuciyata ke tafasa da na ganki sai inji ta yi sanyi. Kece karin kumallo na, ko da na ci abinci in banji muryarki ba yunwa bata sakina. Taba waya akwai dadi amma ni hira dake yafi min dadi. Ko a indiya sai an bincika kamin a samu me kyau irin naki. Bansan akwai mata masu kama da larabawa ba a kasar mu sai da na hadu dake. Bincikena ya kare ban gano mace me kwarjini irin naki ba. Kanshinki na kai ni Duniyar da ban tantance ba. Nasan 'Ya'yanmu zasu zama kyawawa saboda mun dace da juna. Na yi babbar sa'a idan na sameki a matsayin mata, dan kuwa 'ya'yana zasu samu tarbiyya. Hankalinki da nutsuwarki na kara sawa in soki. Kina da kamun kai, kina da girmama mutane, kin iya kalaman soyayya, Allah yawa...