Monday, January 13
Shadow

Tarihi

Sunan fir’auna na gaskiya

Tarihi
Babu tsayayyar magana akan ainahin sunan Fir'auna wanda suka yi zamani da Annabi Musa (A.S). A Qur'ani dai an bayyana mana sunansa da fir'auna, saidai masana tairihi na zamani, sun bayyana cewa, sunan Fir'auna, sunan sarautane a kasar Misra/Egypt, akwai ainahin sunansa na gaskiya. Majiyoyi da yawa sunce sunan Fir'auna na gaskiya shine MUSAB BIN WALID. A turance kuma, Masana Tarihi da yawa sun ce sunan sa, Ramesses II Saidai wasu kalilan sun ce sunansa Seti I. Ko ma dai menene sunansa, abin sani shine la'anannen Allah ne, wanda yayi mulki da zalunci wanda kuma karshensa wuta. Allah ne mafi sani.
Karanta jadawalin makarantun sakandare guda 114 da suka fi dadewa a Najeriya ko makarantarku na ciki?

Karanta jadawalin makarantun sakandare guda 114 da suka fi dadewa a Najeriya ko makarantarku na ciki?

Tarihi
Wadannan jadawalin makarantun sakandare guda 114 ne wanda suka fi dadewa a Najeriya, ko makarantarku na ciki? 1. CMS Grammar School, Bariga, Lagos (1859)2. Methodist Boys High School, Victoria Island, Lagos (1878)3. Methodist Girls High School, Yaba, Lagos (1879)4. Baptist Academy, Obanikoro, Lagos (1885)5. Hope Waddell Training Institute, Calabar (1895)6. St. Anne’s School, (Old Kudeti Girls’ School) Ibadan (1896)7. Oron Boy’s High School, (Old Oron Training Institute) Oron (1897)8. Wesley College of Science (old Wesley College), Elekuro, Ibadan (1905)9. St. Paul’s College, Iyenu, Awka (1900)10. Methodist Boy’s High School, Oron (1905)11. Abeokuta Grammar School, Idi-Aba, Abeokuta (1908)12. King’s College, Catholic Mission Street, Lagos (1909)13. St. John’s School, Bida (1909)14. Alhud...
Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa

Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa

Siyasa, Tarihi
Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa. A ranar 8 ga watan Yuni 1998 Allah Ya yi wa tsohan shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, Janar Sani Abacha rasuwa; Yau shekara ashirin da shidda da ke nan. Da Wadanne Irin Ayyukan Alheri Ku Ke Tunawa Da Shi? Allah Ya Jikansa Da Rahama! Daga Jamilu Dabawa
Ina ake buga kudin nigeria

Ina ake buga kudin nigeria

Kasuwanci, Tarihi
Kanfanin Nigerian Security Printing and Minting (NSPM) ne ke buga kudin Najeriya. Kuma kamfanin na zaunene a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. A baya dai akan kai Kwangilar buga kudin zuwa kasashen waje amma a zamanin Mulkin Shugaba Buhari, an buga kudin na Naira a Najeriya. Saidai a duk sanda aka buga sabbin kudi, 'yan Najeriya kan yaba inda wasu ke kalubalantarsu, musamman ma dai ta bangaren ingancin Kudin.

Wacce jahace asalin hausa

Tarihi
Jihar Katsina itace tushen Hausa. Garin Daura dake jihar Katsina shine tushen Hausa. Anan ne aka samu labarin bayajidda. Saidai duk da haka wasu masana musamman na zamani suna karyata cewa Akwai labarin bayajidda. Hakanan wasu na tantamar cewa Daura ce tushen Hausa. Akwai masu ganin cewa, Jihar Kano itace tushen Hausa. Sannan akwai masu ganin cewa jihohin Kebbi, Zamfara da Sokoto ne Tushen Hausa. Abin tabbatarwa kawai shine, Jihohin Arewa maso yamma sune Asalin Hausa wanda anan ne Hausawa suka fi yawa. Akwai Hausawa a kasashen Nijar, Kamaru, Chadi, Central Africa Republic da sauran wasu kasashen da ba za'a rasa ba.

Matan shehu ibrahim inyass nawane

Tarihi
Kana da tambayar matan shehu ibrahim inyass nawane? Mafi ingancin amsa itace, matan Shehu Ibrahim Inyass 4 ne. Akwai wasu ikirare-ikirare dake yawo cewa ya auri mata sama da 4 amma mafi ingancin bayani shine matansa 4 ne. Daga ciki kuwa akwai 'yar Najeriya, Sayyada Bilqis wadda 'yar jihar Kogi ce. Akwai kuma sayyada Fatimatou, sai kuma Sayyada Afiyatou, Akwai kuma Sayyida A'isha wadda rahotanni suka bayyana cewa, itace babba a cikin matan nasa. Hakanan wasu rahotanni sun bayyana cewa 'ya'yansa 75, kuma ya rasu yana da shekaru 75, hakanan ya wallafa litattafai 75. Saidai wasu rahotannin sun ce 'ya'yansa 100 kuma ba'a tantance iya yawan litattafan da ya rubuta ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa: A shafin twitter zaku same mu a @hut...