Tuesday, December 31
Shadow

Wasanni

A wannan satin ake sa ran Manchester United zata kori Ten Hag

A wannan satin ake sa ran Manchester United zata kori Ten Hag

Kwallon Kafa, Labaran Manchester United
A wannan satin da muke ciki ake sa ran Kungiyar Manchester United zata kori me horas da 'yan wasanta Erik Ten Hag. Thomas Tuchel ne dai ake tsammanin zai maye gurbin Ten Hag a matsayin sabon kocin United. Tuni kuma har Thomas Tuchel ya gana da wakilin Manchester United, Sir Jim Ratcliffe Tuchel ya bayyana cewa idan aka bashi aikin horas da Manchester United, zai dawo da Jadon Sancho zai kuma yi aiki da Mason Mount.
Bidiyo: Kalli Yanda wasan Rangers da Enyimba ya kare cikin hayaniya, Magoya baya suka cika filin wasan

Bidiyo: Kalli Yanda wasan Rangers da Enyimba ya kare cikin hayaniya, Magoya baya suka cika filin wasan

Kwallon Kafa
Wasan Rangers da Enyimba ya kare cikin tashin hankali bayan da alkalin wasan ya baiwa Rangers bugun daga kai sai me tsaron raga ana kusa da tashi wasan. 'Yan Enyimba dai sun fice daga filin inda hakan ya jawo magoya baya suka cika filin ya hargitse. Kalli Bidiyon a kasa. https://www.youtube.com/watch?v=S2ME11vlABs?si=54C9RceD2gC5A0WD
Real Madrid ta fi kowace kungiya kyau a Duniya>>Inji Messi

Real Madrid ta fi kowace kungiya kyau a Duniya>>Inji Messi

Kwallon Kafa, labaran messi na yau, Wasanni
Tauraron dan kwallon MLS kuma tsohon dan wasan Barcelona, Lionel Messi ya bayyana cewa, Kungiyar Real Madrid ta fi kowace kungiya Kyau a Duniya. Ya bayyana hakane yayin hirar da aka yi dashi da wata kafa me suna Infobae. Ya bayyana cewa idan sakamako me kyau ake magana, Real Madrid ce kungiyar data fi kowace amma idan kuma iya wasane, ya fi son Guardiola inda yace duk kungiyar da Guardiola ya horas zaka ganda ta yi fice. Yace dan haka iya wasa sai Manchester City amma kuma sakamako sai Real Madrid. Kuma wannan ra'ayi na Messi bai zo da mamaki ba ganin cewa, Real Madrid ce ta lashe kofin zakarun nahiyar turai.
Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya

Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya

Casemiro, Labaran Manchester United
A wani abin ban mamaki, dan kwallon tsakiya na Manchester United, Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya. Hakanan bayan zuba hannun jarin, a yanzu ya shiga cikin daraktoci masu gudanarwa na kungiyar. Akwai dai tantamar ci gaba da zaman Casemiro a Kungiyar Manchester United indaa ake alakantashi da barin kungiyar. A ranar 3 ga watan Yuni dai an ruwaito cewa, Cristiano Ronaldo ya nemi Casemiro ya koma kungiyar Al nassr su yi wasa tare. Hakanan akwai kungiyoyin Al ahli dana Alqasidiya da suma ke zawarcin Casemiro.
Madrid za ta tattauna da Nacho, Chelsea na zawarcin Sesko

Madrid za ta tattauna da Nacho, Chelsea na zawarcin Sesko

Wasanni
Kyaftin ɗin Real Madrid da ya lashe gasar zakarun Turai, Nacho, mai shekara 34, zai gana da ƙungiyar domin tattauna makomarsa indan kwantiragin ɗan wasan na sifaniya ya ƙare a wannan bazarar. (The Athletic) Chelsea na da ƙwarin gwiwar cewa za ta iya fafatawa da Arsenal a yunƙurin sayen ɗan wasan gaban Slovenia Benjamin Sesko mai shekara 21 daga RB Leipzig. (Standard) Arsenal na nazari kan ɗan wasan Girona da Ukraine Viktor Tsygankov, mai shekara 26, wanda AC Milan ke zawarci. (Sport) Manchester United na sha'awar sayen dan wasan bayan Everton da Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 21, yayin da ta ke neman ƙarfafa ƴan wasanta na baya. Kuma tana zawarcin ɗan wasan baya na Juventus da Brazil Gleison Bremer, mai shekara 27, da ...

YANZU-YANZU: Real Madrid Ta Ci Kofin Zakarun Turai Karo Na 15 Bayan Ta Yi Nasara Kan Dortmoumd Da Ci 2-0

Kwallon Kafa
Kungiyar Real Madrid ta lashe kofi na 15 bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 2-0 a wasan karshe da suka buga a filin wasa na Wembley. Dani Carvajal da Vinicius Jr ne suka ci kwallayen 2. Tsohon dan wasan Real Madrid din kuma kocinta, Zinedine Zidane ne ya kai kofin filin: Kungiyar Borussia Dortmund ta gayyaci Jurgen Klupp ya kalli wasansu. Shine dai ya kaisu wasan karshe na gasar da suka buga a shekarar 2013. Mahaifi da mahaifiyar Jude Bellingham da dan uwansa sun je kallon wasan. https://twitter.com/footballontnt/status/1796957357852832007?t=AfUBdCBVKdBJiz6B_0kChQ&s=19 Hakana mawakin Amurka Jay Z ma ya je kallon wasan: https://twitter.com/ChampionsLeague/status/1796973390743351387?t=l4Xncg675YAq4gnq5hRRRg&s=19 An samu wani da yayi kutse a ...
Hotuna:Cristiano Ronaldo ya kare kakar wasan bana ba tare da kofi ba inda Al Hilal ta doke kungiyarsa ta Al Nassr, Kalli Hotuna da Bidiyonsa yana kuka, Magoya baya suna tsokanarsa ta hanyar kiran sunan Messi

Hotuna:Cristiano Ronaldo ya kare kakar wasan bana ba tare da kofi ba inda Al Hilal ta doke kungiyarsa ta Al Nassr, Kalli Hotuna da Bidiyonsa yana kuka, Magoya baya suna tsokanarsa ta hanyar kiran sunan Messi

Kwallon Kafa, Labaran Cristiano Ronaldo
Kungiyar Al Hilal ta lashe kofin King Cup na Saudi Pro League bayan doke Al Nassr da ci 5-4 a bugun daga kai sai me tsaron gida. Wannan ne kofi na biyu da kungiyar ta lashe a shekaru biyu a jere. Abin bai yiwa Cristiano Ronaldo dadi ba a wasan da aka buga jiya Juma'a a filin wasa na King Abdallah. An kammala wasan Cristiano Ronaldo yana kuka inda abokan wasansa suka rika bashi baki. https://twitter.com/centregoals/status/1796654446396797079?t=IljN_zZoTlKOgbxoo5HmzA&s=19 Da yawa dai sun ce basu taba ganin Ronaldon a cikin irin wannan halin ba. https://twitter.com/WeAreMessi/status/1796788372368699805?t=A6iDAswCtRpc0vRS7MyxFQ&s=19 A yayin da yazo fita daga Filin, magoya bayan Al Hilal sun rika kiran sunan Messi dan su bashi haushi. A karin farko a tari...