Da Asubar yau Juma’a ne aka tashi da mummunan rahotan harin kasar Israyla akan kasar Iran.
Israyla tace ta kaiwa gurare akalla 12 a cikin kasar Iran hare-haren.
Wani abin mamaki shine yanda aka ga jiragen kasar Israyla na shawagi a sararin samaniyar kasar Iran suna ta kai hari inda suke so ba tare da makamai masu kakkabo jirgin sama na Iran sun yi kokarin harbo jiragen ba.
Wasu rahotanni da ba’a tabbatar da su ba amma suna da alamar gaskiya sun ce Israyla ta yiwa makaman kakkabo jiragen sama na kasar Iran Kutse ta hanasu aiki kamin ta kai harin, shiyasa suka kasa harbo jiragenta.
Ana zargin akwai sa hannun wasu munafukai ‘yan kasar Iran da suka bayar da bayanai akan kasar kamin harin.
Wannan Bidiyon na kasa ya nuna yanda Israyla ta jefa makamai masu lalata maboyar karkashin kasa akan tashar sarrafa Urànìyùm ta kasar Iran.
Kafar Wall Street Journal ta ruwaito cewa, Donald Trump a ranar Litinin din data gabata, ya gargadi Benjamin Netanyahu kada ya kaiwa kasar Iràn hari amma yakiya.
Ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasar Amurka bata taimakawa kasar Israyla ba wajan kaiwa Iran wadannan hare-haren ba.
Yace kasarsa na kokarin kare kanta ne kawai da sojojinta inda yace Iran kada ta kaiwa sojojin kasarta hari.
Tuni kasar Iran ta mayar da martani da jirage marasa matuka 100.
Saidai Wasu rahotanni na cewa, Kasar Jordan dama wasu kasashen larabawa na taimakawa kasar Israyla wajan tare wadannan jiragen.
Hakanan rahotanni sun ce kasashen Amurka, Faransa, da Ingila na taimakawa kasar Israyla wajen tare jiragen yakin marasa matuka 100 da Iràn ta jefa mata a matsayin martanin harin da ta kai mata.
Rahotanni daga kasar Israyla sun ce mutane na ta ruguguwar zuwa shaguna dan sayen kayan amfani da yawa dan shirin zaman gida saboda basu san iya tsawon kwanakin da za’a yi ana yakin ba.
Amir Hussein Faqihi daraktan bincike a bangaren makamashin nukiliyar kasar Iran na daga cikin wadanda aka kara ganowa kasar Israyla ta kashe.

Hakanan an tabbatar ta mutuwar masanin kimiyyar Nukiliya me suna Ahmad Reza Dhu al-Faqari.

Daya daga cikin guraren da Israyla ta kaiwa Hari akwai sansanin sojojin kasar Iran.
Hakanan harin ya kashe babban Janar din sojan Iran, Janar Mohammed Bagheri.

Hakanan Shugaban Kula da makamin kare dangin Iran gaba daya watau, Ali Shamkhani ya mutu a harin.

Hakanan Shima Wani Janar me suna General Gholam Ali Rashid an kasheshi a harin:

Bidiyon nan na kasa, Wani gida ne da harin ya lalata:
Hakanan shima shugaban dakarun Revolutionary Guard IRCG, watau Hassan Salami an kasheshi:

Shima Shugaban sojojin saman Iran, Amir Ali Hajizadeh an kasheshi:

Kasar Iran ta musanta cewa an yiwa makaman dake tare hare-haren jiragen samanta kutse.
Hakanan an kashe Dr. Mohammad Mehdi Tehranchi wanda shima masanin kimiyyar Nukiliya ne.

Hakanan an kashe masanin Nukiliya, me suna Dr. Fereydoon Abbasi.
Kasar Jordan ta sanar da tare jiragen sama marasa matuka da kasar Ìràn ta jefawa Israyla a matsayin martanin harin data kai mata.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, A cikin kasar Ìràn Israyla ta tashi jiragenta marasa matuka ta kai mata munanan hare-haren da ta kai mata da safiyar yau.
Rahoton yace Israyla ta yi nasarar dakatar da makaman kariya na kasar Iran.
Hakan ya farune bisa hadin gwiwar wasu munafukai ‘yan kasar ta Iran.
Rahotanni sun ce masu kutse daga kasar Iran sun yiwa kwamfutocin kasar Israyla kutse inda suka hanasu bayar da sakonnin gargadi wanda hakan zai hana ‘yan kasar ta Israyla samun bayanan gargadi kan hare-haren da Iran din ke shirinnkai mata.
Hare-hare 300 ne kasar Israyla ta kaiwa kasar Iran.