Wednesday, January 15
Shadow

Cin Amana: Ji yanda aka kama wani me unguwa yana baiwa ‘yan Bìnďìgà bayanan sirri a jihar Katsina

Hukumar ‘yansandan jihar Katsina ta kama wani me unguwa me suna Usamatu Adamu dake Runka a karamar hukumar Safana saboda baiwa ‘yan Bindiga bayanan sirri.

Kakakin ‘yansandan jihar, Abubakar Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin a yayin da ake gabatar da masu laifin ga manema labarai.

Yace sun samu bayanan me unguwar na da hannu a yin garkuwa da mutane da yawa a jihar.

Yace me unguwar na da hannu a satar wasu mutane kamar haka: Abdulkarim, Malam Sakoa, Malam Sirajo, da Ali, wanda suka ‘yan kauyen na Runka ne.

An kama me unguwar tare da wasu abokan masha’arsa da suka hada da Rabe Sada, wanda aka fi sani da BBC dan shekaru 62, sai kuma Nasiru Sha’aibu dan shekaru 48 wanda dukansu ‘yan kauyen na Runka ne.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan gawarwakin masu garkuwa da mutane birjik a kasa da sojojin Najeriya suka kashe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *