Monday, January 13
Shadow

Cocin Katolika tace yanzu ta amince ‘yan Lùwàdì zasu iya zama limamai a cikin cocin

Cocin Katolika ta yi canje-canje a dokokinta inda tace a yanzu dan luwadi zai iya zama limami a cocin me mukamin Priest.

Saidai cocin tace kamar yadda doka take dolene ya zama ba zai rika yin luwadin ba saboda ba’a yadda Priest su rika saduwa ko wace iri ba.

Wannan sabuwar dokar an yi ta a kasar Italiya ne saidai rahoton yace ba’a sani ko sauran kasashe suma zasu yadda da hakan ba.

Limaman Cocin dai a baya sun yi fama da zarge-zargen luwadi musamman da kananan yara.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tarayya zata sakawa masu samun kudi da yawa sabon Haraji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *