Thursday, February 6
Shadow

Kalli Hotuna: Barayi sun yi yunkurin yin sata a yayin da Gobarar Amurka ke ci

An kama wasu barayi da suka yi yunkurin yin sata a yayin da gobarar garin Los Angeles na jihar California kasar Amurka ke ci.

A yayin da ake neman masu kashe gobara saboda karanci kuma mutane da yawa ke guduwa suna barin gidaje da dukiyoyinsu, wadannan bata gari su kuma sata ce suka sa a gaba.

Zuwa yanzu mutane 4 ne mahukuntan jihar suka fitar da hotunansu a matsayin barayin.

Gobarar dai ta kone gidaje sama dubu goma sha biyu inda masu kashe gobara sama da dubu goma sha hudu ke ta kokarin kasheta.

Karanta Wannan  Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari Ya Ziyarci Birnin Maiduguri Domin Yi Wa Al'ummar Jajen Ibtila'in Ambaliyar Ruwa Da Ta Faru A Kwanakin Baya, Yau Litinin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *