
Ɗan Nijeriya ya zo na 3 a gasar Musabaƙar Al-ƙur’ani ta Duniya
Bukhari Sunusi Idris ɗan asalin jihar Kano da ya wakilci Nijeriya gasar Musabaƙar Al-ƙur’ani ta duniya, ya samu nasarar zuwa mataki na uku, a ɓangaren Izu Sittin da Tafsir. Hakazalika ya samu kyautar Riyal dubu 400, wanda ya kai kwatankwacin Naira Miliyan 160.
Gasar wadda aka gudanar a kasar Saudiyya. Wane fata kuke masa?