Sunday, June 1
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: A Shirye Nike Na Auri Muneerat Abdussalam Idan Har Ta Amince – Inji Usman Ibrahim Kobie

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Matashi Usman Ibrahim Kobie ya bayyana aniyarsa na auren shahararren yar TikTok, kuma mai sayar da maganin ma’aurata, Muneerat Abdussalam idan ta amince.

Matashin ya bayyana haka ne a shafinsa na Manhajar Facebook, a ranar Alhamis.

Inda ya bayyana cewa “Matukar Muneerat Abdussalam ta shirya yin aure, to tazo kawai mu daidaita, ni kuma in aureta in kawota Bauchi cikin farin ciki da natsuwa.

Dama tuni nake da burin auren mace mai hankali da wayewa, wadda ta girme ni a shekarun da kuma tunani, yanzu haka ina da kusan shekaru 30, kuma ina jin cewa lokaci yayi da zan kafa gida na.

Muneerat, ki sani cewa zan baki kulawa da soyayya mai ɗumi, zan ciyar dake, Shinkafa da wake har da ƙwai idan kina so, Kifi mai ƙamshi da lemon tsami, Yoghurt mai sanyi Da Maltina mai cike da kuzari

Karanta Wannan  Yadda Wani Ango Ya Fashe Da Kuka Tare Da Tsugunnawa A Gaban Amaryarsa A Wurin Shagalin Bikinsa

Mu haɗa kai mu rufawa juna asiri, mu riƙa yiwa juna jihadi na soyayya da fahimta kamar yadda nake so mu kasance tamkar sanyi da iska ba rabuwa.” Inji Usman Ibrahim Kobie

Kamar yadda Jaridar Arewa Ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *