Da ɗumi-ɗumi: Ana sarai Erik ten Hag zai sanya sabon kwantaragi a Manchester United nan bada jimawa ba.
Bayan hukuncin INEOS na cigaba da ajiye ten Hag a matsayin mai horas da United, Yanzu shirin ƙungiyar shine ayi gaggawar fara tattauna sabuwar yarjejeniyar tsawaita zaman sa.
Manchester United na son nuna amincewar ta gaba ɗaya akan mai horaswar hakanne yasa zata bashi damar ƙara tsawaita zama a Old Trafford domin a cigaba tafiyar tare.
Tattaunawa tayi nisa, kaɗan ya rage komai ya kammala!
- Fagen Wasanni