DA ƊUMI-ƊUMI: Tun jiya da Safe ba a ga Hamdiyya ba – Inji Lauyanta Abba Hikima.

Tun jiya da karfe 10 na safe ba a ga Hamdiyya ba. Ta fita siyan kayan abinci a cikin garin Sokoto har yanzu ba duriyar ta. Mun sanar da ‘yan sandan Sokoto tun tuni.
YANZU-YANZU: An Sace Ƴar Gwagwarmaya Hamdiya Sidi Dake Rikici da Gwamnatin Sokoto
Da Sanyin Safiyar yau rahotanni dake fitowa daga jihar Sokoto ta bakin Lauyanta Barr Abba Hikima ya bayyana a shafinsa yana mai cewa Tun jiya da karfe 10 na safe ba a ga Hamdiyya ba.
Tun lokacin Ta fita siyan kayan abinci a cikin garin Sokoto har yanzu ba duriyar ta.
Mun sanar da ‘yan sandan Sokoto tun tuni, Inji lauyan na ta.
Hamdiyya Sidi Sharif dai na fuskantar Shari’a tsakaninta da gwamnatin jihar Sokoto bisa zargin kazafi ga gwamnati da Gwamna.