
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewada bai cire tallafin man fetur ba da daukar tsauraran matakai na gyaran tattalin arzikin ba da Najeriya ta talauce.
Yace amma matakan da ya dauka hadi da goyon baya da hakurin da ‘yan Najeriya suka yi masa yasa a yanzu gashi an fara cin amfanin abin.
Yace Farashin kayan abinci ya sauka musamman a cikin watan Ramadana sannan kuma gashi Darajar Naira na ta farfadowa a hankali.
Shugaban ya bayyana hakane a yayin da ya karbi bakuncin ‘yan majalisa da suka yi aiki tare a lokacin yana dan majalisa.
Ya kuma bayyana tsarin Dimokradiyya a matsayin tsari mafi kyawu wanda shine yake kawowa kasa ci gaba.