Friday, April 3
Shadow

Da Duminsa: A karshe dai ICPC sun gano Gidaje na Biliyoyin Naira mallakin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a kasar Egypt

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar yaki da rashawa da cin hanci, ICPC sun gano wasu gidaje a masar Egypt da suke kyautata zaton na Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne.

Gidajen suna a manyan unguwani ne na babban birnin kasar watau Cairo.

Rahotanni sun bayyana cewa darajar gidajen ta fara daga Naira Miliyan 700 ne zuwa sama da Naira Biliyan 5.

Kafar Daily Nigerian ta bayyana cewa wata majiya daga hukumar ICPC ce ta bayyana mata hakan inda ta kara da cewa, suna kokarin ganin sun samu cikakken bayani da zai tabbatar musu cewa gidajen na malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne.

Karanta Wannan  Da Duminsa: EFCC sun kulle gidan da matar Malami, Diyar Tsohon shugaban kasa take ciki

Saidai zuwa yanzu ICPC basu fitar da sanarwa kan hakan a hukumance ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *