
Wasu Rahotanni sun yi zargin cewa kudi aka baiwa Nafiu Bala Gombe da yake ikirarin shine shugaban jam’iyyar ADC har ma ya kai su Atiku Kotu.
Rahotan yace an baiwa Nafiu Naira Biliyan 2 ne ya kawo wannan rikici a cikin jam’iyyar ADC.
Hakanan rahoton yace Nafiu yanzu ya fara buya baya shiga cikin mutane sosai.
A ranar 7 ga watan Afrilu ne dai ake sa ran sake komawa kotu dan ci gaba da shari’ar ta ADC inda ake tsammanin su Atiku zasu nemi kotun ta yi watsi da karar.