Tuesday, May 19
Shadow

Da Duminsa: An bayyana yawan kudaden da ake zargin an baiwa Nafiu Bala dan ya kawo tarnaki a jam’iyyar ADC

Wasu Rahotanni sun yi zargin cewa kudi aka baiwa Nafiu Bala Gombe da yake ikirarin shine shugaban jam’iyyar ADC har ma ya kai su Atiku Kotu.

Rahotan yace an baiwa Nafiu Naira Biliyan 2 ne ya kawo wannan rikici a cikin jam’iyyar ADC.

Hakanan rahoton yace Nafiu yanzu ya fara buya baya shiga cikin mutane sosai.

A ranar 7 ga watan Afrilu ne dai ake sa ran sake komawa kotu dan ci gaba da shari’ar ta ADC inda ake tsammanin su Atiku zasu nemi kotun ta yi watsi da karar.

Karanta Wannan  An samu banbancin ra'ayi: Yayin da Kwankwaso yace masu zàngà-zàngà su bari sai lokacin zabe su canja wanda basu so, Abba Gida-Gida yace yana goyon bayan zàngà-zàngàr kuma ma zai iya shiga a yi dashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *