
Rahotanni daga jihar Filato sun bayyana cewa shahararren Faston nan me magana akan zargin Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya, watau Rev. Ezekiel Dachomo ya kamu da cutar Hanta
Wani dan jarida daga jihar me suna, Masara Kim Usman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta.
Yace Kiristoci su saka Rev. Ezekiel Dachomo a Addu’ar Allah ya bashi lafiya.
Dama dai a baya ya taba kamuwa da cutar inda matarsa ta bashi kyautar daya aka dasa masa, saidai yanzu ciwon ya sake dawowa.