Monday, September 21
Shadow

Da Duminsa: An kama karin sojoji 26 bisa zarginsu da hannu a yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

Rahotanni sun bayyana cewa yawan sojojin da ake tsare dasu ana bincikensu kan zargin hannu a yunkurin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki sun kai 42.

A baya dai rahotanni sun ce sojoji 16 ne aka kama ake bincike.

Saidai a yanzu yawan sojojin sun kai 42 wanda ake bincike kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Jaridar tace wasu majiyoyi a gidan sojin sun sanar da ita cewa, ana gayyatar manyan sojoji inda ake musu tambayoyi game da zargin hannu a yunkirin juyin mulkin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda matar tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke rokon shugaba Tinubu, Kai Uba ne ga kowa dan Allah a sassautawa mijina sharudan beli saboda sharudan da aka saka masa yanzu ba zai iya cika su ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *