Thursday, March 5
Shadow

Da Duminsa: Atiku Abubakar ya kaiwa Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ziyara har gida bayan da aka yi yunkurin kamashi

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kaiwa tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ziyara a gidansa.

Hakan na zuwane bayan da DSS suka yi yunkurin kama ElRufai a filin jirgin sama bayan da ya dawo Najeriya daga Egypt.

Babu dai wani bayani game da ganawar tasu.

Hakan na zuwane bayan da Rotimi Amaechi ya kaiwa ElRufai ziyara har gida inda shima ya nuna masa yana tare dashi.

Karanta Wannan  Juyin Mulki ba zai taba yiyuwa ba a Najeriya inji Maj-Gen. Enenche (rtd)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *