
Majiyoyi da suka haɗa da na gwamnatin jihar Kwara sun tabbatar da cewa an kai harin a wani ƙauye da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Offa, inda a ƴan kwanaki wasu ƴan bindiga suka kai hari a coci wanda ya yi sanadiyya rasa ran mutum biyu sannan suka yi awon gaba da dama.
Hotuna da BBC ta samu daga mazauna garin sun nuna yadda makamin ya faɗa kan gidajen al’umma a garin Offa inda ya rugurguza katangun wasu tsirarun gine-gine.
Wani jami’in gwamnati ya ce al’amarin ya faru a wurare da dama a cikin garin na Offa da suka hada da filin Idi da wasu otal guda biyu da suka hada da Offa Central hotel da Solid Worth Hotel