
Rahotanni daga jihar Naija na cewa akalla Dalibai 50 daga cikin wadanda aka sace daga makarantar St. Mary sun tsere daga hannun ‘yan Bindigar da suka sacesu.
Shugaban kungiyar CAN ta jihar Naija, Bulus Dauwa Yohanna ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, yace Daliban sun kubuta ne ranar Juma’a zuwa Asabar kuma an sadasu da iyayensu.