
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, babu gudu babu ja da baya.
Dokar Haraji tana nan za’a yi ta kamar yanda aka shirya watau nan da 1 ga watan Janairu.
Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Yace Harajin zai kawo ci gaba a Najeriya sosai.