
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad da Takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde sun fasa shirinsu na komawa jam’iyyar ADC.
Rahoton jaridar Punchng ya bayyana cewa, Gwamnonin sun dakatar da aniyarsu ne biyo bayan cite sunayen shuwagabannin ADC da INEC ta yi daga kundin tattara bayananta.
Hakanan Wasu ‘yan majalisar tarayya dake shirin komawa jam’iyyar ta ADC suna sun fasa saboda wannan rikicin da ya mamaye jam’iyyar ta ADC.
INEC ta sanar da cewa, zata jira sai bayan hukuncin kotu kamin su yanke shawara kan shuwagabannin jam’iyyar ADC.