Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Gwamnatin tarayya zata biya ma’aikatan Na-power kudaden da suke bi

Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta ta biyan hakkokin ma’aikatan N-Power har Naira Biliyan 81 da suke bi na aikin da suka yi a tsakanin shekarun 2022 zuwa 2023

Hakan na zuwane bayan wata ganawa ta sirri da aka yi da mataimakin kakakin majalisar Dattijai, Sanata Jibrin Barau ranar Talata, 22 ga watan Yuli.

An yi zamanne tsakanin wakilan ma’aikatan N-Power din da lauyansu, Abba Hikima da kuma ministan jinkai, Nentawe Yilwatda.

A jawabinsa na bayan taro, Sanata Barau ya bayyana cewa, ma’aikatan N-Power din su je majalisa dan nema taimako inda shi kuma ya tuntubi ministan jin kai wanda lamarin ke karkashinsa, yace kuma an samu fahimtar juna.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Motocin dakon man fetur sun fara jigilar man daga matatar Dangote

Yace a zaman tattaunawar an samu ci gaba sosai har ma ma’aikatan N-Power din sun janye karar da suka shigar a kotu.

Ministan ya bayar da tabbacin cewa nan da karshen shekarar 2025 da muke ciki za’a biya kudin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *