
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai zaba a shekarar 2027.
Gwamnan ya bayyana hakane bayan wani zama da aka yi tsakanin sarakunan gargajiya da manyan ma’aikatan gwamnati na jihar da sauran masu ruwa da tsaki.
Gwamnan yace dukansu a jihar sun yanke shawarar goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa a matsayin dansu.
Gwamnan ya bayyana hakane a shafinsa na X.