Wednesday, September 2
Shadow

Da Duminsa: Har yanzu Ina jam’iyyar PDP amma ni da jam’iyyar PDP ta jihata Shugaba Tinubu zamu zaba a zaben shekarar 2027>>Inji Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai zaba a shekarar 2027.

Gwamnan ya bayyana hakane bayan wani zama da aka yi tsakanin sarakunan gargajiya da manyan ma’aikatan gwamnati na jihar da sauran masu ruwa da tsaki.

Gwamnan yace dukansu a jihar sun yanke shawarar goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa a matsayin dansu.

Gwamnan ya bayyana hakane a shafinsa na X.

Karanta Wannan  Sai da Buhari ya amince sannan na bar APC zuwa SD, Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba>>El-Rufai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *