
Da duminsa: Hukumar EFCC na tsare da tsohon gwamnan Sokoto, Tambuwal kan badakalar Naira Bilyan 189.
EFCC TA Garƙame Tambuwal A Abuja
Wakiliyarmu Khubrah Mustapha Dabai
A halin yanzu dai tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal yana hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a hedikwatarta da ke Abuja.
Ana yi wa Tambuwal tambayoyi ne kan zarge-zargen fitar da makudan kudade da suka kai Naira biliyan 189, wanda aka bayyana a fili cewa yin hakan ya saɓawa dokar halatta kudaden haram, ta shekarar 2022.
Majiyarmu ta talabijin ta tattaro cewa tsohon gwamnan ya isa ofishin EFCC ne da misalin karfe 11:30 na safe, inda aka kai shi gaban kwamitin bincike kan badakalar kuɗaɗen.
Duk ƙoƙarin da Dimokuradiyya Tv ta yi har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya ki cewa komai kan binciken da ake yi.
Dimokuradiyya
Efcc
#Tambuwald