Friday, December 26
Shadow

Da Duminsa: Hukumomi a jihar Sokoto sun ce akan farar Hula Khàrìn Amurka ya fada

HARE-HAREN AMURKA A SOKOTO: Ba mafakar ’yan ta’adda aka kai wa hari ba kusa da Asibiti harin ya fada –inji Dan Majalisar yankin Hon. Bashar Isah

Daga Ayau News

Dan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto mai wakiltar Tambuwal ta Gabas yankin da abun ya faru, Hon. Bashar Isa Sarkin Yakin Jabo, ya musanta ikirarin cewa akwai mafakar ’yan ta’adda a yankin Jabo, inda aka ce sojojin Amurka sun kai hari a daren Alhamis.

Ayau News ta ruwaito a hirarsa da DCL, Hon. Bashar ya ce wurin da abin ya faru kusa da Asibitin Jabo PHC ne, yankin da al’umma ke zaune lafiya, ba cikin daji ba, kuma babu wani bayani da ke nuna ayyukan ’yan ta’adda a yankin.

Karanta Wannan  Facebook zai kori ma'aikata dubu uku

Ya kara da cewa bayan harin, jama’ar yankin na cikin fargaba da tsoro, ganin cewa ba su san inda abin makamancin haka zai sake faruwa ba. Ya jaddada cewa ba a kai hari kan wajen da ake zargin ’yan ta’adda suke ba, a cewarsa.

Amma dai za a jira hukumomi su gama tabbatar da yankin da aka kaiwa harin domin tabbatar da cikakken bayani akan lamarin

Me zaku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *