
Rahotanni daga jihar kano na cewa, hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC ta gano wata masana’antar hada ababen fashewa ko ace bama-bamai a Kwakwaci Kano.
An gano lita 88,560 ta kemil daban-daban da ake amfani dasu wajan hada ababen fashewa irin su bamabamai a Kano.
Shugaban hukumar, Prof. Mojisola Adeyeye, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Fagge, Kano.
Daraktan Bincike na hukumar, Dr Martins Iluyomade ne ya wakilceta a wajan binciken inda yace bai taba ganin tarin kemikal a waje guda ba irin wanda ya gani a Kanon.
Yace irin wannan kemikal sai mai bada shawara ga shugaban kasa kan harkar tsaro ya amince ake shigo dashi cikin kasa yace kuma irin wannan da suka gani zai iya tayar da gaba dayan Kano idan aka hada ababen fashewa dashi.
Yace amma me kemikal din ya tsere mamallakin dakin ajiyar ne kawai suka kama amma suna kokarin kama mamallakin kemikal din.