
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya na shirin kakaba dokar ta baci da dakatar da gwamnonin jihohin Benue da Zamfara saboda matsalar tsaro.
Tuni majalisar tarayya ta aikewa wadannan jihohi da majalisunsu wasikar gayyata kan su je su yi bayanin dalilin da zai hana kada a saka dokar tabaci a cikin jihohin nasu.
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama me suna Guardians of Democracy and Rule of Law ce ta aikewa majalisar tarayya da bukatar hakan.
Kungiyar tace Gwamnonin wadannan jihohi sun kasa samar da tsaro ga al’ummarsu inda ta nemi majalisa ta kai dauki wadannan jihohin.
Majalisar dai ta tabbatar da aikewa da wannan bukata.