
Kotun tarayya dake Abuja ta bayar da belin Tsohon Ministan kwadago, Chris Ngige.
Hakan na zuwane duk da kin amincewa da bayar da belin da EFCC ta yi.
Ana zargin Chris Ngige da bayar da kwagila wadda ta zarta naira Naira Biliyan 2 da bata kamata ba a karkashin sa lokacin yana minista.