
Rahotanni daga Abuja na cewa kotu ta tasa keyar tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige zuwa gidan yarin kuje saboda zargin bayar da kwangiloli da suka kai na Naira N2,261,722,535.84 ba bisa ka’ida ba.
An zargeshi da aikata laifuka 8 amma duk ya ki amsa laifinsa.
Kotun tace a ajiyeshi a gidan yarin kuje kamin nan da ranar 14 ga watan Disamba sanda za’a a saurari bukatar neman belinsa.