Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Kungiyar kwadago ta NLC ta fasa zanga-zanga kan karin kudin kiran waya

Kungiyar kwadago ta NLC ta fasa yin zanga-zanga data shirya kan karin kudin kiran waya da kaso 50.

A ranar Talata ne dai Kungiyoyin na kwadago da sauran na fafutuka suka shirya zanga-zanga dan nuna adawa da wannan kari.

kungiyoyin sun bayyana dakatar da zanga-zangar ne bayan ganawa da wakilan Gwamnatin tarayya a ranar Litinin a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya a Abuja.

Shugaban kungiyar kwadagon Joe Ajaero yace sun dakatar da zanga-zangar ta yaune saboda gwamnati ta amince ta kafa kwamiti na musamman da zai duba kowane bangare dan samar da mafita akan lamarin.

Karanta Wannan  Hotuna: Yadda sabuwar ƙungiyar 'yan tà'àddàn (Lùkùràwà) da ta ɓulla a yankin Sokoto da Kebbi suka kashe mutane kimani 15 a ƙauyen Mera da ke Jihar Kebbi bayan sun yi ɗauki ba daɗi da 'yan ƙauyen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *