Friday, February 7
Shadow

Babu maganar tattaunawa, ba zamu rage ko sisi a karin kudin kiran da muka yi ba>>Kamfanonin Sadarwa Irin su MTN, Airtel suka bayyana

Kungiyar kamfanonin sadarwa ta bayyana cewa babu wani abu da zai sa su rage karin farashin kudin kiran waya da kaso 50 da gwamnati ta amince musu.

Kamfanonin sun nemi yin karin kaso 100 bisa 100 amma hukumar sadarwa ta NCC ta amince musu da yin karin kaso 50 cikin 100.

Wannan karin ne yasa kungiyoyin fafutuka suka ce basu amince dashi ba dan zai saka mutane a cikin wahala.

Saidai shugaban kungiyar masu kamfanonin sadarwa ta Najeriya Gbenga Adebayo yace ba zasu rage ko sisi a cikin kaso 50 din da suka kara ba.

Yace ragin zai zama kamar mutum ne dake bukatar numfashi amma a ki bashi, yace muddin ana son ci gaba da samun sabis me karfi da dorewa da kuma kara fadada ayyukansu to sai an bari an yi wannan kari.

Karanta Wannan  Daya daga cikin matan da mutuminnan na kasar Equatorial Guinea yayi lalata dasu kuma Bidiyon lalatar ya bayyana ta kàshè kanta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *