Friday, February 7
Shadow

Da Duminsa:Shugaba Tinubu ya amince da kafa jami’ar Kimiyyar Muhalli a Ogoni jihar Rivers

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa kudirin dokar kafa jami’ar kimiyyar Muhalli a Ogoni dake jihar Rivers, Niger Delta.

Shugaban ya sakawa dokar hannu ne a fadarsa dake Abuja da yammacin ranar Litinin.

Shugaban yace wannan babbar nasara ce a kokarin Najeriya wajan kawo ci gaban muhalli, Ilimi, da ci gaba me dorewa.

Yace wannan jami’a na nuni da cewa gwamnati ta damu da ci gaban al’ummar yankin gaba daya inda yace shekaru da yawa mutanen yankin na ta fafutukar ganin sun samawa kansu mafita ta bangaren gyaran muhalli.

Shugaban ya kuma jinjinawa majalisar tarayya bisa kokarin amincewa da wannan kudirin dokar.

Karanta Wannan  Shekararsa 70 Amma Aikinsa Shine Baiwa Masu Gaŕkuwa Da Mutane Bayanan Sirri

Ya kuma jawo hankalin masu ruwa da tsaki da suka hada da matasa, iyaye, da masu zaman kansu da su goyawa wannan jami’a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *