
Kungiyar kwadago ta NLC ta fasa yin zanga-zanga data shirya kan karin kudin kiran waya da kaso 50.
A ranar Talata ne dai Kungiyoyin na kwadago da sauran na fafutuka suka shirya zanga-zanga dan nuna adawa da wannan kari.
kungiyoyin sun bayyana dakatar da zanga-zangar ne bayan ganawa da wakilan Gwamnatin tarayya a ranar Litinin a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya a Abuja.
Shugaban kungiyar kwadagon Joe Ajaero yace sun dakatar da zanga-zangar ta yaune saboda gwamnati ta amince ta kafa kwamiti na musamman da zai duba kowane bangare dan samar da mafita akan lamarin.